DA NA SANI ƘEYA CE…: Mun kori PDP da kamfen ɗin ‘CANJI’ mu na cike da jahilcin halin da Najeriya ke ciki a 2015 -Farouk Adamu

Ɗaya daga cikin jiga-jigan jam’iyyar APC, Farouk Adamu Aliyu ya bayyana cewa daga baya sun fahimci cewa sun ƙirƙiro salon ‘canji’ a kamfen ɗin zaɓen 2015 alhali su na cike da duhun jahilcin gaskiyar lamarin halin da Najeriya ke ciki a lokacin.

Aliyu wanda tsohon Ɗan Majalisar Tarayya ne da ya wakilci Ƙananan Hukumomin Birnin Kudu da Buji na Jihar Jigawa a ƙarƙashin ANPP, ya yi wannan furuci ne a lokacin da ake tattaunawa da su uku a gidan talabijin na Channels, ranar Alhamis a Abuja.

An yi tattaunawa mai zafi da wasu mashahuran ‘yan siyasar Arewa uku, a lokaci guda.

Baya ga Farouk Aliyu, akwai Usman Bugaje, ɗaya daga cikin waɗanda su ka fito da sabuwar jam’iyya kwanan nan tare da Attahiru Jega, domin su kori APC da PDP.

Akwai kuma Umar Arɗo, jigo a PDP, kuma tsohon ɗan gwagwarmayar Buhari kafin ya zama shugaban ƙasa.

Farouk Aliyu ya yi iƙirarin cewa a lokacin da su ke ƙoƙarin kamfen ɗin yaƙin neman zaɓen 2015, sun bijiro da wasu alƙawurran da sai daga baya su ka fahimci ashe a lokacin ba su da masaniyar halin da ƙasar nan ke ciki.

Shugaba Buhari ya yi alƙawarin samar da tsaro, amma a lokacin mulkin sa tsaron ya ƙara muni sosai musamman Arewa maso Gabas da Arewa ta Tsakiya.

“Yanzu misali, kafin zaɓen 2015 duk mun fito kan titi mun yi zanga-zangar tsadar fetur da neman a cire tallafin man fetur.

“To a gaskiyar lamari mun yi wannan zanga-zangar a cikin jahilci. Saboda kuwa sai daga baya mu ka fahimci akwai halin da tilas sai an riƙa biyan kuɗaɗen tallafin man fetur ga manyan dillalan da ke shigo da shi.” Inji Farouk Aliyu.

“Ka san akwai abin da mutum kan yi a cikin jahilci, ko kuma ya aikata abin domin ɓata wa wani suna kawai.”

Tsohon ɗan majalisar kuwa hamshaƙin manomi a yanzu, Farouk ya ce Buhari bai kasance ɗan takarar da ya fi kowa cancanta ba a zaɓen 2015. Ya ce shi dai ne tsarin zaɓe ya fi nuna wa yatsan kamata ya yi a tsayar da shi.

Da ya ke magana a kan cin hanci a rashawa kuwa, wanda a kamfen ɗin APC aka yi alkawarin za a kawar a Najeriya, cewa ya yi har yanzu ana cin hanci da rashawa da satar kuɗin gwamnati a wannan mulki na APC.

“Ba za a ce a yanzu ba a yi ba. Ana cin hanci da rashawa da satar kuɗin gwamnati a wannan mulkin. Sai dai ba a iya fitowa muraran ana tinƙahon ana yi, kamar yadda aka riƙa yi a zamanin mulkin PDP.”

Da aka taɓo batun tsayar da ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 mai zuwa, Farouk ya ce babu wata matsalar da ta dabaibaye APC wajen fito da ɗan takarar ta.