Gwamnatin Kaduna bata ce za ta rusa ofishin ƙungiyar ƴan jarida na Kaduna ba – Shugaban Ƙungiyar

Shugaban ƙungiyar Ƴan jarida reshen jihar Kaduna, Adamu Yusuf ya karyata rahoton da ake yaɗawa wai gwamnatin Kaduna za ta rusa ginin ofishin ƙungiyar dake titin Muhammadu Buhari.

” Abinda muka sani shine, gwamnatin Kaduna ƙarkashin hukumar raya birane na jihar, ta aiko mana da takardar cewa lallai mu gyara fasalin shagunan dake kewaye da ginin ofishin mu saboda ya saɓa wa yadda dokar gine-gine ta jihar.

Yusuf ya ce shine abinda muka sani. ” Babu inda gwamnati ta ce za ta rusa ginin NUJ a Kaduna inda take magana akai shaguna ne kuma tuni mun zauna da su, har kungiyar ta fara ɗaukar mataki kadin wa’adin da gwamnatin jihar ta saka

Hukumar raya birane na jihar ta aika wa ƙungiyar takardar cewa su gyara fasalin shagunan dake kewaye da ofishin kungiyar waɗanda mallakin kungiyar ne ko kuma ta rusa su ta gyara da kanta.

Wannan takarda ya sa wasu suka rika yaɗa rahoton cewa wai gwamnatin jihar za ta rusa ginin NUJ a Kaduna.