DA ƊUMI-ƊUMI: Gwamnan Bauchi ya sauƙe Kwamishinoninsa

Raba a Facebook

Tura zuwa Twitter

Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Muhammad ya sanar da rushe majalisar Kwamishinoninsa tare da sauƙe daukkan masu riƙe da mukaman siyasa da suka haɗa Sakataren gwamnatin jihar da shugaban ma’aikatan gidan gwamnati da masu bashi shawara da mataimaka na musamman.

A cikin wata sanarwar manema labarai da Kakakin Gwamnan Mukhar Giɗaɗo ya fitar a safiyar Laraba, Gwamnan ya ce sauƙe muƙarraban gwamnatin bai shafi masu bashi shawara a kan harkokin tsaro da harkokin majalisun jiha da tarayya da zuba jari da yaɗa labarai ba.

Gwamna ya umarci dukkan Kwamishinoni da su miƙa ragamar gudanar da ofisoshin su ga manyan sakatarorin ma’aikan su tare ajiye dukkan abin da suka san na gwamnati ne.

Sanarwar Manema Labarai.