Najeriya ta fara ƙera manyan wayoyin hannu

Raba a Facebook

Tura zuwa Twitter

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya rantsar da sabbin kwamishinonin hukumar ƙidaya ta ƙasa da hukumar kula da ma’aikatan gwanatin tarayya.

Ya rantsar da sabbin Kwamishinonin ne kafin fara zaman majalisar zartarwa ta ƙasa da ya saba jagoranta mako-mako a fadar gwamnati ta Aso Rock Villa dake babban birnin tarayya Abuja.

A yayin rantsarwar, kamfanin HMTI ya gabatar wa shugaba Buhari da sabon samfurin farko na wayar Salula ƙirar Android da aka ƙera ta a Najeriya a karon farko a tarihin Najeriya.

Shugaban kamfanin, Otumba Niyi Adebayo ne ya jagoranci tawagar kamfanin domin gabatar da sabon safurin kamfanin.