Trump ya taya Najeriya murna kan matakin da Buhari ya ɗauka akan Twita

Raba a Facebook

Tura zuwa Twitter

Tsohon shugaban Amurka Donald J. Trump ya taya Najeriya murnar dakatar da shafin Twitter bisa goge wasu rubutun shugaban ƙasa Buhari.

Trump ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata.

A cewarsa, “Ina yi wa Najeriya murnar haramta amfani da Twitter saboda shafin ya haramtawa shugaban Najeriya amfani da shafin.

Trump na daga cikin manyan mutane a duniya da Twitter ta fara dakatarwa bisa ƙaryata sakamakon zaben Amurka da ya sha kaye bayan duniya ta tabbatar da sahihancin zaben.