DA ƊUMI-ƊUMI: An dakatar da aiyyukan hukumar ZAROTA a Zamfara

Raba a Facebook

Tura zuwa Twitter

Gwamnan Jihar Zamfara Muhammad Bello Matawalle ya dakatar da dukkanin ayukkan hukumar ZAROTA a fadin jihar.

Hakan ya biyo bayan sa’insa da aka samu tsakanin jami’an hukumar ZAROTA da direbobin mayan motoci a safiyar yau a birnin Gusau wanda ya janyo manyan motoci suka rufe babban mashiga da fita babban birnin jihar.

A sanarwar dakatarwar da ta fito daga ofishin babban Sakataren sashen gudanarwa na gwamnatin jihar Alhaji Yakubu Sani Haidara, ta ce an dakatar da dukkan aiyyukan hukumar a halin yanzu.

A cewar sanarwar, Gwamna Muhammad Bello Matawalle ya umarci jami’an haɗin gwiwa na hukumomin ƴan sanda, VIO da Road Sefiti da su ci gaba da gudanar da aikin hukumar tare da bada umarni a kafa kwamitin da zai binciki ainihin abin da ya faru.

Daga ƙarshe an nemi al’umma da su kasance masu bin doka da oda.

Tun da safiyar Alhamis Hausa Daily Times ta kalli wani Bidiyo dake nuna yadda manyan motoci suka cushe babbar hanyar Lalan wadda ita ce babban mashiga da mafita babban birnin jihar Gusau ta Zamfara.

Wani dirrban ɗaya daga cikin manyan motoci da suka cushe hanyar kuma ya bayyana abin da ya janyo rufr hanyar, ya ce jami’an hukumar ne suka tilasta wani direban babbar mota biyan taran N50,000 ba tare da sanin abin da ya aikata ba.