DAƘA-DAƘAR AYYUKAN TASHOSHIN RUWA: Kotu ta dakatar da kwangilar da su Minista Amaechi suka yi wa ‘kiran sallah da garaya’

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta dakatar da gagarimar kwangilar aikin saka na’urorin kula da jigilar manyan jiragen ruwa masu dakon kaya zuwa tashoshin ruwan Najeriya.

Wata Kungiyar Kare Haƙƙin Jama’a da Tattalin Arziki mai suna ‘Citizen Advocacy, Social and Economic Right’ (CASEN) ce ta shigar da ƙara, inda ta yi zargin cewa an karya doka wajen bayar da kwangilolin na maƙudan biliyoyin kuɗaɗe.

Kwangilar dai an bayar da ita ga kamfanoni biyu, waɗanda ko a wani rahoto da Premium Times Hausa ta buga a farkon Nuwamba, ta nuna cewa kamfanonin ba su cancanci a ba su kwangilar ba, amma a haka Ameachi ya kai wa Buhari sunayen su, shi kuma ya sa hannun amincewa.

Kamfanonin su ne MedTech Scientific Limited da Rozi International Limited.

Ƙungiyar CASEN dai ta maka Ministan Harkokin Sufuri, Rotimi Amaechi ƙara, shi da Antoni Janar, kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami. Sai kuma Hukumar Tantance Kuɗaɗen Kwangiloli (BPE), sai kuma kamfanonin biyu da aka bai wa kwangilolin.

Mai Shari’a D.U Okorowo ya umarci Minista Ameachi da BPE su dakatar da kwangilar. Su ma kamfanonin biyu su daina kiran kan su waɗanda aka bai wa kwangilar, har sai kotu ta yanke hukuncin idan sun cancanci a ba su kwangilar ko ba su cancanta ba.

Mai Shari’a ya ce za a ci gaba da sauraren shari’ar a ranar 12 Ga Janairu, 2022.

Salsalar Yadda Rikicin Gagarimar Kwangilar Tashoshin Jiragen Ruwa Ta Ruƙume Daga Teku Zuwa Kotu:

Wannan baban labari ne mai ɗauke da cikakken bayanin yadda Buhari da Amaechi suka gabji kwangilar aikin tashoshin jiragen ruwa, su ka garka wa malaman tsafta da dillalan gidaje.

Shugaba Muhammadu Buhari da Ministan Sufuri Rotimi Amaechi sun karya ka’idoji da dokokin sharuɗɗan bayar da kwangila, inda su ka ɗauki kwangilar maƙudan kuɗaɗe ta aikin da ya shafi killace bayanan tsaro a Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa, suka bai wa kamfanonin da kwata-kwata ba aikin su ba ne, hanyar jirgi daban, ta mota daban.

Kamfanin da aka bai wa kwangilar dai bai san komai a harkar ayyukan tashoshin jiragen ruwa ba. Aikin kamfanin kawai shi ne kwangilar kayan ayyukan lafiya.

Zai yi kwangilar tare da wani kamfanin haɗin-guiwa, wanda shi kuma aikin sa shi ne dillanci da gina manyan rukunin gidaje kawai.

Tuni dai Hukumar Tsntsncewa da Duba Cancantar Kwangila da Cancantar Ɗan Kwangila (BPE), ta ce wannan lamari da ya faru abin kunya ne da zubar da kuma da mutunci. Sannan kuma ta ce kwangilar haramtacciya ce, amma babu yadda hukumar za ta iya yi, tunda Shugaba Buhari ne da kan sa ya karya ƙa’ida, ya sa hannun amincewar a bai wa kamfanonin da ba su dace kuma ba su cancanta ba kwangilar.

Waɗannan bayanai duk PREMIUM TIMES ce ta bankaɗo su, kamar yadda za ku karanta hujjojin da za a bijiro da su a ƙasa.

Wannan katafariya kuma haramtacciyar kwangila ta jefa manyan jami’an gwamnatin Buhari cikin yanayin jifar juna da habaice-habaicen zargi.

Ita kuwa Hukumar BPE wadda aka karya ƙa’idojin da ta shimfiɗa, aka ɗauki kwangilar aka bai wa kamfanonin da ba a tantance ba, tuni ta rubuta takarda ta rashin jin daɗi, wadda a fakaice kawai takardar wadda PREMIUM TIMES ta gani, ta na nuna cewa Buhari da Amaechi sun karya doka da ƙa’ida, inda su ka ɗauki aikin garambawul ɗin keke su ka bai wa wanda ko ɗaure ƙararrawar keken ma bai iya ba.

Binciken PREMIUM TIMES dai ya dogara ne da wasiƙun da su ka riƙa karakaina, waɗanda ke ɗauke da umarnin Shugaban Ƙasa da umarnin Amaechi da kuma irin martanin da Hukumar BPE ta riƙa maidawa, inda ta ke nuna rashin dacewar da aka nuna, inda aka ƙi bin ƙa’ida.

An Karya Dokar Bada Kwangiloli Ta 2007 -BPE:

Hukumar da ke kula da tantance cancantar adadin farashin kwangila da cancantar kamfanin da za a ba kwangilar, wato Bureau for Public Procurement (BPP), ta ce an karya sharuɗɗa da ƙa’idojin da doka ta gindaya a Dokar Bada Kwangiloli ta 2007.

Aikin kwangilar da ake magana an bayar ɗin dai shi ne aikin yin amfani da na’urorin da ke nunawa ko iya gane duk inda wani jirgin ruwa ɗauke da kaya ya ke (ICTN) idan ya shigo Najeriya da kuma wanda zai fita ko ya fita daga Najeriya.

Wannan aiki ne mai samar da maƙudan kuɗaɗen haraji a ƙasa, idan aka yi shi kamar yadda doka ta tanadar. Sannan kuma aiki ne da ya shafi batutuwan tsaron ƙasa.

Wata wasiƙa da Ma’aikatar Harkokin Sufuri ta aika wa BPE a ranar 26 Ga Agusta, 2021, ta ce a yanzu za a ci gaba da aikin ICTN, wanda gwamnatin baya ta dakatar.