An kashe manoma 45 a Jihar Nasarawa -Fadar Shugaban Ƙasa

Aƙalla manoma 45 ne aka kashe a rikice-rikicen da su ka shafi manoma da makiyaya a ƙananan hukumomin Lafiya, Obi da Awe na cikin Jihar Nasarawa.

Fadar Shugaba Muhammadu Buhari ce ta bayyana adadin mutanen da aka kashe ɗin, a cikin wani saƙon ta’aziyya da jimami da Kakakin Yaɗa Labarai na Buhari, Garba Shehu ya fitar.

Babu cikekken bayanin yadda faɗace-faɗacen suka faru. Amma dai ganin yadda Shehu ya bayyana cewa “manoma 45 ne aka kashe”, hakan ya nuna kenan rikicin manoma ne da makiyayan da ke ɗauke da muggan makamai.

“Shugaban Ƙasa ya kaɗu sosai da jin mummunan labarin kisan manoma 45 a jihar Nasarawa. Abin takaici ne matuƙa.

“Ya na miƙa ta’aziyya ga iyalan mamatan, tare da jajanta waɗanda aka ji wa rauni. Kuma ya na ƙara jaddada cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da kare rayukan jama’a.”

Buhari ya miƙa ta’aziyyar sa ga Gwamnatin Jihar Nasarawa, tare da jinjina mata, ganin yadda ta yi gaggawar kai ɗaukin tallafi da agajin gaggawa ga iyalan waɗanda abin ya shafa.