ƘUDIRIN GYARAN DOKAR ZAƁE: Matakin da za mu ɗauka tunda Shugaban Ƙasa ya ƙi sa wa dokar hannu -Gbajabiamila

Kakakin Majalisar Tarayya Femi Gbajabiamila ya bayyana irin mataki da Majalisar Tarayya za ta ɗauka, ganin cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya ƙi amincewa ya sa wa Ƙudirin Gyaran Dokar Zaɓe Hannu.

A ranar Lahadi ce dai wa’adin kwana 30 su ka ya cika, domin Buhari ya sa wa dokar hannu ko ya ƙi.

Tun cikin watan Nuwamba aka aika masa da ƙudirin. Sai ranar Talata ce Buhari ya aika wa Majalisar Dattawa da Majalisar Tarayya cewa ba zai sa wa ƙudirin hannu ba, saboda batun zaɓen kai-tsaye na ‘yar-tinƙe.

Kakakin Majalisar Tarayya ya ce tunda hutun wata ɗaya za a tafi, Majalisar Tarayya za ta jira sai ta dawo daga hutu sannan ta ga abin da ya fi dacewa ga ƙasar nan.

“Ko ma dai me kenan, kada mu bari garin gyaran doro mu karya ƙugu. Ƙasar nan ce mafi muhimmanci a gare mu.”

A nasa bayanin, Shugaban Marasa Rinjaye Ndudi Elumelu, ya bada shawarar Majalisa ta gaggauta cire batun zaɓen-kai-tsaye a cikin ƙudirin gyaran zaɓen, sai a sake aika wa Buhari a ranar Talata ɗin kafin lokacin tashi aiki, yadda shi Buharin tilas ya sanya wa dokar hannu.

PREMIUM TIMES ta buga labarin iƙirarin da Sanata George Sekibo na PDP ya yi cewa, sama da Sanatoci 73 sun rattaba hannun kafa sabuwar dokar zaɓe ta hanyar bijire wa Buhari.

Sanata George Sekibo ya tabbatar da cewa akwai sama da sanatoci 73 waɗanda su ka sa hannun amincewa su tirsasa Shugaba Buhari su tabbatar da Sabuwar Dokar Zaɓe, wadda Buhari ya ƙi rattaba wa hannu domin ta zama doka.

Sekibo ya ce waɗanda suka rattaba hannun sun fito ne daga jam’iyyu daban-daban, kuma ana sa ran sake samun ƙarin wasu da dama.

Sekibo ya nuna damuwar sa a kan don me Buhari zai ƙi yarda a kafa dokar yin zaɓen-kai-tsaye na ‘yar-tinƙi a zaɓukan shugabannin jam’iyyu.

“Najeriya fa ba ƙasar mutum ɗaya ba ce, kuma ba wani kamfanin mutum ɗaya ba ne, ballantana ya ce sai abin da ya ga dama zai yi a kamfanin sa.

“Doka ta ba mu ikon kafa dokar, ko da Buhari bai amince ba, matsawar sanatoci da ke don a kafa ta sun kai kashi 2 bisa 3 na Sanatocin da ake da su 109.

“Sashe na 54 (4) da na 54 (5) ne ya bai wa sanatoci wannan ƙarfin ikon kafa dokar, duk da shugaban ƙasa bai yarda ba.”