CUTAR MONKEY POX: Alamomi da abubuwan da za a kiyaye don guje wa kamuwa da cutar – Hukumar Lafiya Ta Duniya

Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta bayyana wasu hanyoyi da mutane za su kiyaye domin kauce wa kamuwa da cutar Monkey Pox.

Shugaban kwamitin dakile yaduwar cututtuka a hukuma, Rosamund Lewis ta bayyana cewa cutar ta fi yaduwa idan ana yawan zama kusa da wadanda suka kamu da ita.

Alamun cutar sun hada da zazzabi, rashin kasala a jiki, kumburin gaɓaɓu, fesowar ƙuraje da sauran su.

Ana kuma iya kamuwa da cutar idan mutum ya yi jima’i da wannda ya ke ɗauke da cutar.

Ta yi kira ga mutane da a yi gaggawar zuwa asibiti a duk lokacin da aka ga alamun citar ya bayyana a jikin mutum.

Rosamund ta yi kira ga masu ruwa da tsaki da gwamnatoci da su tsananta wayar da kan mutane game da hanyoyin samun kariya da gujewa kamuwa da cutar domin dakile yaduwar cutar.

Daga ranar 13 zuwa 26 ga watan Mayu mutum 257 ne suka kamu da cutar a kasashe 23 dake karkashin kungiyar duniya WHO.

Kasar UK ta fi fama da yaduwar cutar inda mutum 106 suka kamu, Portugal – 49 da Canada – 26.

A Najeriya mutum 46 ne suka kamu da cutar daga Janairu zuwa Afrilu 2023, kasar Kamaru na da mutum 25 da suka kamu mutum 9 sun mutu daga Disemba 2021 zuwa daya ga Mayu 2022.

Dakile yaduwar cutar Monkey Pox

WHO ta ce za ta kara zage damtse wajen dakile yaduwar cutar a kasashen da cutar ta bullo.

Kungiyar ta Kuma ce ta tanadi maganin rigakafin cutar karambau domin yi wa mutane allurar rigakafin cutar a kasashen da cutar ta bullo.

Ta ce akwai kuma wani maganin rigakafin cutar karanbau da kasashen Canada da Amurka ke amfani da shi Mai suna Modified vaccinia Ankara Bavarian Nordic strain ko kuma MVA-BN wanda duk za a hada ana amfani da su domin dakile yaduwar cutar.