TAKARAR SHUGABAN ƘASA: Okorocha ya garzaya an tantance shi, bayan ya ƙwaci kan sa da belin naira miliyan 500 a kotu

Ɗan takarar shugaban ƙasa a APC, kuma tsohon Gwamnan Imo, Rochas Okorocha, ya samu nasarar tantancewa a gaban Kwamitin Tantance ‘Yan Takarar Shugaban Ƙasa na APC, a Abuja.
Ya garzaya wurin tantancewar bayan cika sharuɗɗan belin kan sa da Naira miliyan 500 a kotu.
Okorocha ya isa Otal ɗin Transcorp Hilton da misalin ƙarfe 9:30 na dare, a ranar Talata.
Tun da rana dai Babbar Kotun Tarayya ta Abuja ta bada belin sa kan Naira miliyan 500, bisa sharaɗin cewa a ci gaba da tsare shi sai ya cika sharuɗɗan belin tukunna.
An nemi ofishin rajistara na kotu ya tabbatar da kadarar da za a bayar a matsayin beli, kuɗin ta ya kai Naira miliyan 500 ɗin.
Baya ga sharuɗɗan beli, an ƙwace fasfo ɗin Okorocha, an hana shi fita daga Najeriya.
Okorocha ya shaida wa manema labarai cewa kai-tsaye daga Hedikwatar EFCC ya ke.
Okorocha ya ce ya amince da a tsayar da ɗan takara bisa yarjejeniya, ba tare da an yi zaɓe ba. Amma ya ce a tabbatar kowane ɗan takara ya amince da yin haka ɗin.
A ranar Talata ce dai Shugaba Buhari ya nemi gwamnonin APC su bar shi ya zaɓi ɗan takarar da ya ke so ya gaje shi.
Sai dai kuma a ranar Talata ɗin ce aka tantance Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbajo.
Tun a ranar Litinin ce dai APC ta tantance ‘yan takara 22, saura 11
ASHAFA MURNAI
Kwamitin Tantance ‘Yan Takarar Shugaban Ƙasa na APC ya tantance ‘yan takara 12 a ranar Litinin.
Kwamitin wanda ke ƙarƙashin shugabancin tsohon Shugaban APC na Ƙasa, John Oyegun, ya ware ranakun Litinin da Talata domin aikin tantancewar da ake yi a babban ɗakin taron otal ɗin Transcorp Hilton, Abuja.
Waɗanda aka rigaya aka tantance sun haɗa da:
Emeka Nwajiuba, Davida Umahi, Felix Nicholas, Ibekunle Amosun, Gwamna Badaru Abubakar, Sanata Ajayi Borroffice da Ken Nnamani.
Sauran sun haɗa da Uju Ken-Ohaneye, Rotimi Amaechi, Ahmed Yerima da Bola Tinubu.
Dukkan su dai kowane ya bayyana irin tasirin sa da cancantar sa da kuma irin ci gaban da ya ce zai samar wa ƙasa.
An tantance Tinubu a lokacin da wata ƙungiya ta rubuta takardar rashin cancantar sa fitowa takarar shugaban ƙasa, domin a cewar ƙungiyar, ya na da takardun shaida waɗanda ba su cancanci tsayawar sa takarar ba.
A yau Talata ne kuma za a tantance sauran, ciki har da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, Rochas Okorocha da sauran su.
Sai dai kuma ba a sani ba ko Babbar Kotun Tarayya za ta bayar da belin Okorocha kafin a kai ga lokacin tantance shi.
PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa ba a ga gilmawar tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan a wurin tantancewar ba a ranar Litinin.
Jonathan ya ƙaurace wa dandalin tantance ‘yan takarar APC.
Jam’iyyar APC mai mulki ta fara aikin tantance ‘yan takarar shugaban ƙasa, bayan tsaiko na makonni biyu da aka samu.
A yanzu haka dai ana tantancewar a otal ɗin Hilton, Abuja.
Tun da farko dai an tsara za a yi aikin tantancewar a ranakun 14-15 Ga Mayu, amma sai aka ɗaga zuwa ranar 23 Ga Mayu.
Daga nan kuma an sake ɗagawa zuwa 29 da 30 Ga Mayu, yayin da kuma aka ɗaya Gangamin Zaɓen Takarar Shugaban Ƙasa zuwa 6 zuwa 8 Ga Mayu.
Duk da an hana ‘yan jarida shiga zauren tantancewar, an ruwaito cewa za a tantance ‘yan takara ne su 23, ciki har da Bola Tinubu da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbajo da kuma Rotimi Amaechi.
Yayin da Jonathan ya ƙi karɓar fam ɗin da wata ƙungiya ta ce ta sai masa, hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta yanke shi ne Jonathan na da ‘yancin sake tsayawa takara a zaɓen 2023.
Sai dai kuma yayin da ake tantance ‘yan takarar APC a yau Litinin a Abuja, har yanzu ba a ga wulgawa ko giftawar Jonathan a wurin tantancewar ba.
A halin yanzu dai Jonathan ya na ƙasar Italiya wurin taron Ƙungiyar haɗin guiwar Afrika da Gabas ta Tsakiya.