Comment on Ko Buhari ya amince yayi Takara a 2019 ko mu maka shi a kotu – Ganduje by Shamsu habibuj

Gwamnnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya fadi cewa a shirye suke da su maka shugaban kasa Muhammadu Buhari a Kotu idan yace ba zai yi takara a karo na biyu ba.

Ganduje ya bayyana haka ne bayan ganawar da jam’iyyar APC reshen jihar Kano tayi inda ta tsayar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin dan takaranta a zaben 2019.

Wadanda suka halarci taron sun hada da duka shugabannin kananan hukumomi 44 na jihar da mataimakan su, ‘yan majalisar jihar 34 da wasu jiga-jigan jam’iyyar a Kano.

Kakakin fadar shugaban Kasa Garba Shehu ya ce Buhari ya ji su amma bai ce Eh ba bai ce A’a ba.

Gwamnan jihar Jigawa Mohammed Badaru ya halarci taron.