Comment on TARON PDP: Lema ta yage a taron PDP na yankin Arewa Maso Yamma, Namadi Sambo ya fice a fusace by Mahmoud Suleiman, (iyan kagarko),

A ranar jajibirin gangamin jam’iyyar PDP da za a gudanar yau Asabar a Abuja, sai ga wani sabon rikici ya tirnike reshen Arewa-maso-maso yamma na jam’iyyar inda aka yi zargin yin karfa-karfa wajen dora ‘yan takara mukamai.

Taron da masu ruwa da tsakin jam’iyyar na wannan shiyya su ka yi a jiya Juma’a, a gidan tsohon jakadan Najeriya, Aminu Wali, an tashi baram-baram, har ta kai tsohon shugaban kasa Namadi Sambo ya fice daga taron a fusace, tun kafin lokacin tashi.

An amince cewa wannan yanki ne zai samar da Sakataren Jam’iyya na Kasa da kuma Shugabar Jam’iyya ta Kasa, sai kuma Mataimakin Ma’aji na Kasa, har da Mai Bayar da Shawara Kan Al’amurran Shari’a.

PREMIUM TIMES ta gano cewa manyan iyayen jam’iyyar na wannan shiyya, ciki har da jagoran su Aminu Wali, sun bukaci a samu matsaya guda ta yadda za su fito da wadanda za a zaba ta hanyar maslaha, ba sai an kai ga yin zabe ba.

Sai wani mai suna Sani Mashi ya ce hakan ba zai yiwu ba, domin kowane dan takara ya kashe kudi ya sayi fam, kuma an tantance shi. Don haka a bar dimokradiyya ta yi aikin ta.

Mashi dai ya fito ne takarar mataimakin mai bayar da shawara kan al’amurran shari’a.

Ya kara da cewa da a cewa sun janye wa mutum daya, har gara a ce mutum dayan ya kayar da su a Dandalin Eagle Square zurin zabe.

“Maimakon su tuntube mu tun tuni tukunna, amma sai an zo karshe su ce wai umarni suka ba mu, saura su janye wa wani? Haba!”

“Wannan kiki-kaka ce ta janyo har tsohon mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo ya fice daga taron a fusace.” Inji Sani Mashi.

Wasu da suka halarci taron, sun hada da Ibrahim Shekarau, Attahiru Bafarawa, Sule Lamido, Ibrahim Shema da Ramalan Yero.

Akwai kuma Kabru Turaki, Bello Halliru, Danjuma Laeh, Bello Hayatu Gwarzo, Ibrahim Sharu, Ibrahim Tsauri, Nenadi Usman, Baraka Sani da Sauran su.

An ce kuma masu neman su yi wa ‘yan takara karfa-karfa, sun kasa cimma nasarar dora Sanata Ibrahim Tsauri a matsayin dan takarar Sakataren Jam’iyya na Kasa, bisa sauran ‘yan takara da suka hada da: Abubakar Mustapha da Nenadi Usman.

Haka ita ma Baraka Usman daga Kano, an nemi ta janye wa “wata kifin-rijiya” mai suna Mariya Bala Waziri”, amma Baraka ita ma ba ta janye din ba.

Haka kuma an ki yarda a janye wa Wada Masu daga takarar Mataimakin Ma’ajin Jam’iyya na Kasa. Masu dai shi ne jami’in da ke wa Aminu Wali ‘yan buge-bugen takardu a ofishin sa. Haka daya daga cikin wanda ya halarci taron ya shaida wa PREMIUM TIMES.