Ahmed Musa ya ƙara aure a karo na uku

Raba a Facebook

Tura zuwa Twitter

Fitaccen ɗan wasan ƙwallon kafa a duniya kuma Kaftin na ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta ƙasa Super Eagles Ahmed Musa ya ƙara aure.

Musa wanda wannan shine auren sa na uku, ya rabu da matarsa ta farko Jamila a shekarar 2017 wanda nan take ya maye gurbinta da Juliet kuma suke tare har yanzu.

A halin yanzu sabuwar amaryar tasa, Maryam ita ce matarsa ta biyu.

Babban jarumi a masana’antar Kannywood Ali Nuhu ya wallafa a shafinsa na Instagram yana Musa murna.