CIKAR WA’ADIN AFKA WA NIJAR: Nijar ta haramta wa jiragen kowace ƙasa keta sararin samaniyar ta

Shugaban ECOWAS kuma Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya sake kiran taron gaggawa na ECOWAS, domin a sake tattauna matsalar juyin mulkin Nijar.
Za a yi taron ne a Abuja, bayan cikar wa’adin kwanaki bakwai da kungiyar ta bai wa sojojin mulkin Nijar su sauka ya cika, amma ba su sauka ɗin ba.
Wannan ne zai kasance taron ECOWAS na biyu tun bayan da sojojin juyin mulki su ka hamɓaras da gwamnatin Shugaba Mohammed Bazoum daga kan mulki.
A taron farko ne dai ECOWAS ta ƙaƙaba wa Nijar takunkumi daban-daban, ciki kuwa har da na afka mata da ƙarfin soja, da niyyar maida mulki a hannun farar hula, kuma ga wanda su ka hamɓaras, wato Bazoum.
Yayin da wa’adin ya cika a ranar Lahadi, ana cikin zaman zulumin sauraren matakin da ECOWAS za ta ɗauka, sai aka sanar da sake taron ECOWAS a ranar Alhamis mai zuwa.
Lamarin ya zo yayin da akasarin ‘yan Arewacin Najeriya ke nuna rashin amincewa a kai wa Nijar farmaki.
Haka ita ma Majalisar Dattawan Najeriya ta ƙi amincewa da buƙatar da Tinubu ya sanar da ita cewa sojojin Najeriya za su jagoranci na ECOWAS, domin a kai wa Nijar hari.
Shirye-shiryen Ko-ta-kwana: Nijar Ta Hana Jiragen Kowace Ƙasa Keta Sararin Samaniyar Ta:
Yayin da wa’adin ECOWAS ya cika a ranar Lahadi, Jamhuriyar Nijar ta bada sanarwar hana jiragen kowace ƙasa keta sararin samaniyar ta.
Sojojin mulkin Nijar sun bayyana “rufe sararin samaniyar ƙasar har sai yadda hali ya yi.”
Nijar ta yi gargaɗin cewa duk wani yunƙuri, ganganci ko izgilancin da ya kai wata ƙasa ta keta mata doka, to za ta sha ragargaza da ƙarfin tsiya.”
Majalisar Tsaron Cikin Gidan Nijar wadda ta ƙunshi Janar-janar ɗin da su ka ƙwace mulki ta yi haka ne saboda akwai ƙishin-ƙishin ɗin kai mata hari daga wasu ƙasashen Afrika ta Tsakiya guda biyu. Sai dai ba ta ambaci sunayen ƙasashen biyu ba.
Faransa Ta Hana ‘Yan Ƙasar Ta Shiga Nijar, Burkina Faso Da Mali, ƙasashen da su ka ƙwace mulki cikin 2022 da 2020.
Sasantawa Ta Hanyar Diflomasiyya Ce Kaɗai Hanyar Da Ta Dace – Jamus Da Italiya:
Su kuma ƙasashen Jamus da Italiya sun yi kira ga ECOWAS su ƙara tsawaita wa’adin sauka daga mulkin da ECOWAS ta bai wa mahukunta sojojin Nijar. Sannan kuma sun ce. Haka dai Minsitan Harkokin Wajen Italiya, Antonio Tajani ya shaida wa jaridar La Stampa.
Shi ma Ministan Harkokin Wajen Jamus cewa ya yi “mu na fatan dai tattauanawa ta fannin diflomasiyya za ta yi nasarar dawo da tsarin dimokraɗiyya a Nijar.”
Mali Da Burkina Faso Za Su Nijar Domin Nuna Wa Ƙasar Goyon Bayan Su:
Ƙasashen Mali da Burkina Faso sun bayyana cewa a ranar Litinin mai zuwa za su tura tawagar haɗin-guiwa zuwa Nijar, domin nuna cikakken goyon bayan su ga gwamnatin mulkin ƙasar.
Gaggarimin Gangamin Goyon Bayan Mulkin Soja A Nijar:
A ranar Lahadi, ranar da wa’adin ECOWAS ya cika, an gudanar da gagarumin taron nuna goyon baya ga mahukuntan mulkin sojan Nijar.
Tutar ƙasar Rasha ce aka riƙa dagawa a wurin taron, wanda Shugaba Mulkin Soja na Nijar, Janar Tchiani da kan sa ya halarta.