Sharri ake yi min, ban tsara wa Kotun Zaɓen Ƙararrakin Shugaban Ƙasa hukuncin da za ta yanke ba – Fashola

Tsohon Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde, ya ƙaryata zargin da yanzu haka ke yawo a soshiyal midiya cewa ya tsara wa Kotun Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa irin hukuncin da aka a za yanke a shari’ar da Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na LP suka maka Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu.
Fashola ya kuma yi kira ga sashen tsaron da abin ya shafa su gaggauta binciko waɗanda suka yi masa wannan sharri, domin a hukunta su.
Cikin wata sanarwa da Kakakin Yaɗa Labaran Fashola, Hakeem Bello ya fitar, tsohon Ministan ya nuna ɓacin matuƙa dangane da ƙazafin da ya ce ake ta watsawa a kan sa.
Yayin da ya ke ƙara bayyana zarge-zargen da cewa duk labaran bogi ne, Fashola ya ƙara da cewa shi ya daɗe ma ba ya Abuja, ballantana a ce har sojoji sun dira, sun yi masa ƙawanya a gida.
Ya yi tir da masu watsa wannan ƙazafi a kan sa, ya na mai cewa abu ne mai hatsarin gaske.
“Tuni Fashola ya ma fara shirye-shiryen maka gidan jaridar da ta watsa bayanan a kotu, wato shafin X da kuma Hukumar Sadarwa ta Ƙasa, NCC.
“Ya kuma roƙi jami’an tsaro su ɗauki batun da matuƙar muhimmanci.”
Ya ce wannan ƙage da sharrin da aka yi masa wani shiri ne kawai na tsoma wa dimokraɗiyya ƙafar-ungulu a ƙasar nan, domin kawai a kawo koma-baya ga ribar da aka samu daga dimokraɗiyya a Najeriya.