KAMEN YAN KWAYA A ABUJA: An kam Kwayoyin maskewa 57,450 hannun ma su sha da safarar su

Hukumar hana sha da safarar muggan kwayoyi ta kasa NDLEA ta kama muggan kwayoyi da suka hada da tramadol, rohypnol da exol-5 57,450 a hanyar Abaji zuwa Abuja a hannun wani mai safarar su mai suna Joseph Usman.
Kakakin rundunar Femi Babafemi da ya sanar da haka a wata takarda da ya fitar a Abuja ya ce rundunar ta kama Usman da kwalaben maganin tari na kodin 4,082.
Babafemi ya ce rundunar ta kama Usman a wata mota da ta taso daga Onitsha jihar Anambra zuwa Abuja ranar Juma’an da ya gabata.
Bayan ‘yan sanda sun kama kwayoyin ‘Dextromethorphan’, Methamphetamine, Dimethyl Sulfone da wiwi za a kai su kasashen Turai.
Babafemi ya ce dakaru sun gano kwayar ‘dextromethorphan’ da aka hada da hodar ibilis gram 272 a cikin wasu sarkunan wuya za a kai Greece, ganyen wiwi gram 665 da aka boye a cikin kwalin sabulun ‘Dudun Osun’ za a kai su kasar Hong Kong
Ya ce kwayar Dimethyl Sulfone gram 261 da aka boye cikin gashin doki za a kai New Zealand Sannan Shima kwayar ‘Methamphetamine’ kg 1.5 za a kai kasar New Zealand.
A jihar Kano ‘yan sanda sun kama wata mata mai suna Ladi Peter mai shekara 47, Umar Salisu mai shekara 38, Ahmed Naheeb dan shekara 36, Ibrahim Umar dan shekara 42 da Musa Suleman mai shekaru 43 bisa ga laifufukan da suka jibanci safarar muggan kwayoyi.
Babafemi ya ce an kama wadannan mutane da kilo gram 977.7 na ganyen wiwi.
Ya ce an kama wadannan mutane a hanyar Zaria zuwa Kano da hanyar Kwanar Dangora ranar Juma’ar da ta gabata .
Babafemi ya ce rundunar ta kama kilo gram 2,445 na ganyen wiwi a hannun wani Usman Nar dake Madinatu a karamar hukumar Jere ranar biyar ga Agusta.