Buhari zai tafi ƙasar Faransa

Fadar shugaban ƙasa ta fitar da sanarwa ta hannun kakakinta Malam Garba Shehu cewa shugaban ƙasa Muhammafu Buhari zai tafi Faransa a ranar Lahadi domin halartar wani taron ƙasashen Afrika kan halin da tattalin arziƙin su ya shiga, biyo bayan bullar annobar Korona tare da neman mafita musamman kan irin yawan bashin da ake binsu wanda yake daɗa taruwa.

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zai shafe kwanaki huɗu yana wannan ziyara ta aiki.

Taron zai gudana a birnin Paris karƙashi jagorancin shugaban Faransa Emanuel Maccron, wanda zai samu halartar manyan bankunan duniya da wasu shuwagabannin ƙasashen duniya. Za a tattauna akan yadda za a samar da tallafin kuɗaɗe daga waje tare da yadda za a kula da basuka da ake bin ƙasashen Afrika da kamfanoni.

A yayin taron kamar yadda sanarwar ta zo, Buhari zai gana da shugaba Macron domin tattaunawa kan matsalolin tsaro dake addabar yankin Sahel da Tafkin Chadi daidai sauransu.

Har wayau, sanarwar ta ce Buhari ba zai dawo ba sai ya smau ganawa da kushoshin duniya a harkar Man Fetur da Gas da manyan injiniyoyi da masana harkokin sadarwa tare da majalisa da wakilan tarayyar turai da ma ƴan Najeriya mazauna Faransa.

Shugaba Buhari zai tafi tare da Ministar Kuɗi Zainab Shamsuna, Ministan harkokin Waje Geoffrey Oyema, Ministan Ciniki da Masana’antu Otunba Adeniyi Adebayo, Ministan Lafiya Osagie Ehanire.

Saura sun haɗa da Mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro(NSA) Babagana Munguno, Shugaban hukumar leƙe asiri ta Najeriya (NIA) Ambasada Ahmad Rufa’i Abubakar