ZAFTARE MA’AIKATAN KADUNA: Barazanar kungiyar kwadago ba zai tsorata mu ba – Gwamnatin El-Rufai

Gwamnatin jihar Kaduna karkashin gwamna Nasir El-Rufai ta bayyana cewa barazanar kungiyar Kwadago na shirin fara yajin aiki a jihar ba zai tsorata ba ko kuma ya sa ta janye ahirinta na zaftare ma’aikatan jihar da take da niyyan yi.

Mutanen jihar Kaduna za su shiga cikin matsanancin hali daga ranar Asabar a dalilin umarni da kunguiyar kwadago ta bada na ma’aikata su fara yajin iki na gama gari a jihar Kaduna.

Hakan ya biyo bayan gargadi da kungiyar ta baiwa gwamnatin jihar ta janye daga shirin korar ma’aikata da ta yi niyyar yi tunda wuri ko kuma gaba daya tun daga Abuja a yo mata gangami har sai ta dakatar da wannan nufi na ta.

Kamar yadda sanarwar ya kunsa, daga ranar Asabar din yau, kungiyar ta umarci, kada jirgin sama ya sake tashi daga filin sama na Kaduna, jirgin kasa ya dakatar da ayyukan sa kaf a jihar.

Haka kuma Hukumar rarraba wutar lantarki ta kasa, ita ma ta tabbata ta kashe wutan lantarki da ake sha a duk fadin jihar har sai illa ma sha’Allah.

” Wannan gargadi ne mai mahimmanci. Da mai’aikata da hukumomi duk gaba daya kaf ba za su yi aiki a Kaduna ba daga yau Asabar. Babu wuta, babu sufurin jirgin sama da na kasa, komai zai tsaya cak da yau Asabar har sai El-Rufai ya dakatar da shirin korar dubban ma’aikatan jihar.

‘Yan Kaduna dai sun ga tasko, domin a halin da ake ciki gwamnati ta ce taji ta gani, shege ka fasa.

Martanin gwamnati

” Muna kira ga kungiyar kwadago su shiga taitayin su, kada su kuskura su kawo mana rudani da tashin hankali a Kaduna.

” Matsayar gwamnati na nan daram dam, babu gudu ba ja da baya. Ma’aikata ne tabbas sai mun rage su. Ba za mu rika kashe kusan duka kudaden jihar wajen biyan ma’aikatan da jihar bata bukata ba., Sannan wasu su ce mana dole sai mun bi yadda suke so.

” Tun a shekarar 2020, ma’aikata dake kasa da mataki 14 suke gida. Wadanda a lallai ana bukatar su kuma suna aiki. Haka kuma yan siyasan da muka nada, wasu da yawa ba su mana komai, duk zamu sallame su, domin samun kudaden da za a yi wa talakawa aiki.

” Mun samu labarin cewa wasu za su shigo Kaduna domin kawo wa jihar cikas da sunan yajin aiki. Mun sanar da jami’an tsaron jihar cewa akwai wasu da ke shirin tada zaune tsaye a jihar da sunan wai yajin aiki. Suna su su kawo mana cikas a wasu wuaren ayyukan mu da suka hada da asibitocin mu da makarantu.

Gwamnatin Kaduna ta ce ba za ta janye daga yadda ta tsara ayyukan ta ba, musamman wajen rage ma’aikatan jihar dake zaman kashe wando suna amsar albashi ba su yin komai.