Kungiyar Ma’aikatan Kotu sun watsa wa gwamnonin goron gayyatar janye yajin aikin da su ka aika masu

Kungiyar Ma’aikatan Kotuna da Sassan Gudanar da Shari’a na Najeriya (JUSUN), sun bijire wa kudirorin da gwamnonin Najeriya su ka shimfida a matsayin yadda za su bai wa bangaren kotuna da shari’a cin gashin kai, domin su janye yajin aikin kaurace wa harkokin shari’a ya da addabi kasar nan.

A cikin tayin da gwamnonin su ka bijiro wa JUSUN, sun bukaci Gwamnatin Tarayya ta kafa Kwamitin Asusun Kula da Kudaden Jihohi (SAAC), wanda zai rika sa-ido kan kudaden da ake bai wa bangarori uku masu tafiyar da gwamnati a kowace jiha.

To amma a wata takardar bayan taro da JUSUN ta raba wa manema labarai a ranar 8 Ga Mayu, sun ki yarda da batun da gwamnonin Najeriya su ka bijiro da shi.

JUSUN ta jajirce cewa lallai kudaden da ake bai wa bangaren shari’s da kotunan jihohi, su rika fitowa kai-tsaye daga hannun gwamnarin tarayya, zuwa hannun shugabannin bangarorin kudade na fannonin shari’a.

JUSUN ta kara fa cewa kudaden su biyo ta Hukumar Kula da Fannin Shari’a ta Kass (NJC).

Ta ce ta na nan kan bakan ta lallai a bi tsarin da dokar kasa ta gindaya, wadda Shugaba Muhammadu Buhari ya sa wa hannu, amma gwamnonin su ka sa kafa su ka yi fatali da dokar.

JUSUN ta ce ba za ta bari a sa gatari a sare doka, ko a sa aska a yi mata saisaye, ko a canja wa doka wasu kamannu ba.

“Matsayar da mu ka ka cimma ita ce a bi doka kawai.”

Idan ana so JUSUN ta janye yajin aiki har kotuna su ci gaba da gudanar da shari’u ka’in da na’in, to a cire dukkan kudaden bangaren shari’u da kotuna na jihohi tun daga na Oktoba, 2020 zuwa na watan Mayu daga aljihun gwamnatin tarayya kai-tsaye, a biya su ta hannun Hukumar NJC, kada a damka wa gwamnoni.” Inji JUSUN.