Buhari ya umurci Gwamnan CBN, Emefiele da jami’an gwamnati da ke takarar kujerun siyasa su ajiye aiki

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emefiele da duk wani minista ko jami’in gwamnati da ke takarar shugaban Kasa, gwamna ko majalisar jiha da na kasa, ya ajiye aiki nan da ranar 16 ga Mayu.
Shugaba Buhari ya fadi haka ne a wata wasika da sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ya fitar ranar Laraba bayan an tashi taron kwamitin zantaswa ta ƙasa a Abuja.
A wasikar shugaba Buhari ya ce duk ministan dake takarar kujerar siyasa za su mika aiki ga karamin ministan ko kuma babban sakataren ma’aikatar su kuma su kama gaban su.
Zuwa yanzu ministan kimiya da fasaha Ogbonnaya Onu, ministan Neja-Delta Godswill Akpabio da karamin ministan ilimi Chukwuemeka Nwajiuba duk sun ajiye aiki.