ƁATANCI GA MANZON ALLAH: Gwamnatin Sokoto ta rufe kwalejin Ilmi na Shehu Shagari

Gwamnatin jihar Sokoto ta rufe Kwalejin Ilimi na Shehu Shagari dake jihar Sokoto.
Hakan ya biyo bayan zargin ɓatanci ga Manzon Allah (SAW) wanda wata ɗaliban makarantar mai suna Deborah ta yi a shafin WhatsApp na ɗaliban makarantar
Ita dai Deborah ta fusata ne wai don wasu ɗalibai sun saka abubuwan addini a cikin guruf din WhatsApp din da suke ciki.
Bayan haka ne sai ta aika da sakon ɓatanci ga manzon Allah SAW a wannan guruf ɗin.
Sai dai kuma ko a lokacin da take yin wannan sako, sai da wata kawarta ta gargaɗe ta cewa waɗannan kalamai bai dace ta yi su kuma kada ta saka a wannan shafin amma kuma ta ki ji.
Dalilin haka ɗalibai suka fusata suka rika bibiyanta suna neman halaka ta amma kuma jami’an tsaro na kare ta domin kada su halakata.
Akarshe sai ɗaliban suka afka mata da jifa da duwatsu rugugi har suka kashe ta.
Gwamnatin Sokoto ta rufe Kwalejin
Gwamnatin jihar Sokoto ta sanar da rufe kwalejin har sai illa mashaAllahu. Sannan kuma gwamna Aminu Tambuwal ya umarci jami’an tsaro su tabbatar da tsaro a yankunan dake kewaye da kwalejin.
Kwamishinan Ilimin Jihar Sokoto Isah Galadanci ya ce gwamna ya umarci ma’aikatar ta gudadar da bincike akai cikin gaggawa.
Haka kuma majalisar masarautar Sarkin Musulmi ta bada sabarwar a bi baasin abin da ya faru sannan a kamo duk waɗanda aka samu da hannu a aikata kisan wannan yarin ya.