Buhari ya dakatar da Hadiza Bala Usman daga shugabar NPA

A wata jibgegiyar baraka da ta kunno kai a ma’aikatar sufuri, wanda ake ta kulle-kulle, da toshe-toshen kada a fallasa, wato a bari ta yadu duniya su sani shine, dakatar da shugaban hukumar kula da tashoshin ruwan Najeriya, Hadiza Bala Usman da shugaba Buhari yayi.

Majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu na takardar dakatar da shugabar tun ranar Talata amma, ba a sanar da dakatarwar ba saboda wasu gaggan yan Najeriya, na bin kafa don tausa Buhari ya janye dakatarwar.

Tuni har shugaba Buhari ya amince babban Darekta a hukumar, Mohammed Bello Koko ya dare kujerar shugabancin hukumar kafin a nada wani sabo.

” Lallai shugaba Buhari ya dakatar da shugabar NPA, Hadiza Bala, amma kuma wasu shafaffu da mai da suke ganin sun isa na can na kokarin ganin Buhari ya janye wannan dakatarwa. Ciki an ce akwai wani tsohon shugaban kasa, da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Ibrahim Gambari da wani tsohon ministan tsaron kasar nan.

Wadannan mutane na kokarin sasanta Hadiza Bala da ministan Sufuri, Rotimi Amaechi wanda rikici ya shiga tsakanin su.

An ce Amaechi ya nemi ta sauka da ga kujerar domin a samu damar gudanar da bincike kan wani zargi da ake mata.

Sai dai kuma ba a fadi ko menene ya shiga tsakanin ta da ministan ba sannan ba a san ko binciken me za ayi ba.

Ana nan dai ana ta boye-boye game da dakatarwar saboda kasa a fallasa, wanda isan har aka yi haka, hukumar ta sanar, to babu sauran hanyar da za abi a dawo da ita.