Yadda ‘yan bindiga suka kashe tsohon dan takarar gwamman Zamfara a titin Abuja-Kaduna suka yi garkuwa da mutane da dama

‘Yan bindiga sun kashe tsohon dan takarar gwamnan jihar Zamfara a zaben 2019, Sagir Hamida.

Yayan marigayin Kabiru Hamida ya sanarwa Kamfanin dillancin Najeriya cewa yan bindigan sun kashe Sagir ne a hanyarsa ta dawowa Gusau daga Abuja bayan hutun karshen mako.

Marigayi Sagir babban dan kasuwa ne a Abuja kuma tsohon ma’aikacin gwamnatin tarayya ne kuma yayi takarar gwamna a Jam’iyyar PDP a 2011.

Bayan rashin nasara da yayi tun a zaben fidda gwani na jam’iyyar, sai ya canja sheka ya koma jam’iyyar APC a 2019 kuma yayi takara a 2019. A wannan lokaci ma bai yi nasara ba, kuma yana daga cikin wadanda suka kalubalanci zaben 2019 a Zamfara.

Daga baya sai ya koma tafiyar tsohon gwamna AbdulAziz Yari bayan gwamnan jihar Bello Matawalle ya canja sheka ya shiga APC daga PDP.

Darektan Yada Labarai na gwamna Matawalle ya ce gwamnan jihar na cike da jimamin wannan rasuwa.

Shafin PRNigeria ya buga cewa wani matafiyi da ya abin ya auku a idon sa kuma ya kubuta ya ce ‘yan bindigar sun tare hanya a kauyen Katari da misalin karfe biyun rana ne.

” Sai da muka koma bayan da muka ji harbe-harben bindiga kuma mun tsaya a wani wuri mai tazara sosai da wurin da al’amarin ya faru. Bayan sa’oi biyu mun ga wasu motoci na bin dayan hanyar, daga nan ne muka ci gaba da tafiya”.

“An yi garkuwa da matafiya da dama ko sun tsere cikin daji saboda munga motoci akalla 15 akan hanya kuma babu kowa a cikinsu lokacin da muka wuce wurin da abin ya auku”, Kamar yadda wannan matafiyi ya shaida PR Nigeria.