BOKO HARAM: Zulum da E-Rufai sun baiwa iyalan marigayi Janar Zirkusu kyautar kudi

Gwamnan Jihar Barno Babagana Zulum ya yi je ta’aziyyar mutuwar Burgediya Janar Dzarma Zirkusu, a gidan sa da ke cikin Barikin Sojoji a Kaduna.

Zulum wanda ya kai ziyarar a ranar Laraba, ya bai wa iyalan marigayin tallafin naira miliyan 20 nan take.

Gwamnan dai ya samu tarba tun a filin jirgin saman Kaduna, daga Kwamishinan Harkokin Tsaro Samuel Aruwan da kuma Kwamandan Garison na Rundunar Soja ta 1, Burgediya Janar T. Opene.

Gwamna Zulum ya tafi da rakiyar Sanatocin Jihar Barno uku, Kashim Shettima, Ali Ndume da kuma Abubakar Kyari.

Sau kuma ‘Yan Majalisar Tarayya biyu, Haruna Mshelia mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Chibok, inda Zirkusu ke Kwamandan Runduna ta 28, da kuma Ahmed Jaha na Ƙaramar Hukumar Askira Uba, inda a can ne Boko Haram suka kashe Zirkusu.

Da ya ke wa Blessing Zirkusu matar mamacin ta’aziyya, ita da ƙanan sa Gurdebil Zirkusu, Zulum ya bayyana cewa mamacin jan-gwarzo ne, kuma rashin sa babban rashi ne ga jihar sa ta haihuwa Barno da kuma Najeriya baki ɗaya.

Nan take Gwamna Zulum ya bada umarnin a ba su naira miliyan 20, domin jajantawa gare su, kuma saƙon ya isa gare su nan take.

A nasa jawabin, Kwamishinan Harkokin Tsaro na Kaduna, Samuel Aruwan, shi ma ya bayyana sanarwar bayar da gudunmawar naira miliyan 2 daga gwamnatin jihar Kaduna.

Ƙanen mamacin Gurdebil Zirkusu da kuma Kwamandan Garison Opene, sun gode wa Gwamna Zulum da sauran ‘yan tawagar sa.