TSADAR RAYUWA: Yadda tsarabar gawayi ta maye tsarabar tsire da balangu, goriba ta maye ƙwan kaji

Idan mutum ya shiga kasuwar Kantin Kwari a Kano, to ƙarshen kallon inda hada-hadar kuɗi kenan. Amma kuma hakan bai hana mutum ya cika da mamakin ganin yadda mutane ke gwaguyar goriba ka-in-da-na-in ba. Kai da ganin akasarin masu cin goribar nan, to ka san cin yunwa su ke yi mata, ba cin marmari ba ne.

Yadda lemun zaƙi da kankana da gwanda su ka Kano, haka goriba ta cika birnin a kasuwanni, unguwanni, lunguna da wuraren taruwar jama’a har ma da ƙananan ‘yan tireda.

A Kano, a yanzu abin da aka fi talla gida-gida shi ne dankalin Hausa, wanda yara ƙanana ke shigowa daga ƙauyuka da sassafe su na talla gida-gida, domin a saya a soya wa yara masu tafiya makaranta, kafin ƙarfe 8 na safe.

Sai dai kuma shi dankali, yara sun fi tallar sa da safe. Abin da aka fi talla daga safe har yamma, ita ce ‘WAYAR MANGAL’. Waya ce ta cikin tayar mota, ake ƙona tayar a cire wayar, ana haɗawa da gawayi ana sayarwa domin a yi girke-girke.

Gawayi Gatan Talaka:

A shekarun baya, idan ka ga magidanci ya koma gida daga kasuwa ko daga neman na abinci, za ka gan shi riƙe da baƙar leda, wadda tsarabar nama balangu ko tsire ne a ciki. Amma yanzu da yawan waɗanda za ka gani riƙe da baƙar leda sun doshi gida, ba tsire ba ne a ciki, gawayi ne.

Yawancin gidaje a Kano an daina amfani da gas, saboda tsananin tsadar da ya yi. Saboda a wasu wuraren kg 1 ya kai naira 800.

“Cikin 2020 ana saida kg 12 naira 3,300. To sai na ke bayar da N3,500 a sayo min, sauran N200 ta sama kuwa, kuɗin mota ne. Amma yanzu N8,500 na bayar makon da ya gabata, aka sayo min kg 12 na gas.” Inji Hajiya Habiba.

Babu unguwar da za ka shiga a Kano ba ka ga wuraren da ake sayar da gawayi ba. Ko dai buhu-,buhu, ko kwano-kwano. Sai fa unguwannin waɗanda ke ci su ƙoshi su yi hidima duk a cikin kuɗaɗen kasafin Najeriya, ko na jiha ko kasafin ma’aikatu da manyan cibiyoyin gwamnati.

Farin ɗango, waɗanda ake ganin annoba ce, to a yanzu sun zama abinci. Idan ma cin marmari ake yi masu, to a gaskiya nema su ke yi su maye gurbin nama. Saboda masu sayarwa ƙulli-ƙulli da kwano-kwano sun yi yawan gaske. Yawan sayar da abu kuwa, alamomi ne da ke nuna cewa akwai yawan masu cin abin.

“To idan ba a ci goriba ba, me za a ci. Ƙwan kajin gidan gona ƙwaya ɗaya a yanzu naira 65 ya ke. Idan ka je teburin mai shayi ka ce a soya maka ƙwai, cewa zai yi naira 80. Kai ni fa abin nan gani na ke kamar wasan kwaikwayon Gidan Badamasi na ke kallo. Anya haka Najeriya za ta ɗore kuwa.” Haka Ali ya shaida wa wakilin mu, a unguwar Jan Bulo.

Irin wannan rayuwa fa ake gayaniya duk gari ko ƙauyen da ka je. Kamar Kano kamar Kaduna da Katsina. Haka abin ya ke a Patiskum ko Panbeguwa.

Babu wani bambanci tsakanin Taraba da Tambuwal. Da Wurno da Warawa duk rayuwar ba sauƙi. Haka Jalingo da Jogana duk hayaniyar iri ɗaya ce. Da Garabawa da Gagarawa duk abin da ya gagari Gambarawa ya gagare su.

Binciken da wakilin mu ya yi ya gano cewa yawancin kayan da ake sayarwa naira 200 cikin 2015 zuwa 2016, yanzu sun kai naira 800. Kwalbar man ƙi babba kuwa ta kai naira 1,000.

Idan mutum na da ɗan rufin asirin sa, shi ma hankalin sa ba a kwance ya ke ba, idan ya yi la’akari da yawan mabaratan da ke kan titi, yawan mabuƙata mata masu sallama gida-gida ɗauke da goyo, janye da ƙananan yara, su na neman ko ƙanzon tuwo ne a ba su, su jiƙa, su ci.

A da da yawa na son zuwa biki cikin birane, domin a je a yi kallon gari, kuma a ci mai daɗi a ƙoshi. A yanzu kuwa tura ta kai bango, mutanen ƙauye da yawa dan za su zo biki birni, daga can za su niƙo garin da za a tuƙa a gidan bikin.

Shin ko akwai wanda zai ce ba a samu canji ba? Amma kuma irin wannan canjin ne aka shafe shekaru 12 ana fafutikar samu?

Bahaushe dai ya ce “jiki-magayi!”