Na siyo hantar biri, kan angulu da kwarangwal ɗin kan zaki a hadamin laƙani – Ɗan damfara

Babbar Kotun Jihar Kwara da ke birnin Ilorin, ta ɗaure wani boka kuma ɗan damfara tsawon shekaru 28 a kurkuku.

An samu Jami’u Isiaka da laifin damfarar wani ɗan Koriya ta Kudu dala $88,521 da ƙaryar zai samar masa kwangila a kamfanin mai na NNPC.

Dala $88,521 ta na kwatankwacin Naira miliyan 30.

Jami’u Isiaka ya riƙa amfani da sunan Kakakin Yaɗa Labarai na Shugaba Muhammadu Buhari Femi Adesina ya damfara.

A ranar Alhamis ce Mai Shari’a Mahmud Abdulgafar ya same shi laifuka huɗu, waɗanda aka ɗaure shi shekaru 7 kowane laifi ɗaya.

Mai laifin ya shaida wa kotu cewa ya yi amfani da wasu kuɗaɗen ya saya wa ɗan Koriya ɗin da ya damfara “kan ungulu, fata da hanjin giwa, ƙungurmin kan zaki da kuma hantar biri.”

Ya ce an yi amfani da waɗanda kayayyakin ne wajen haɗa surkulle, laƙani da tsatsube-tsatsuben neman sa’ar samun kwangilar da ake nema.

A ranar 14 Ga Yuni, 2019 ne dai jami’an EFCC a Ilorin su ka gurfanar da Jami’u Isiaka a kotu.

An zarge shi da yin amfani da sunan Femi Adesina, ya na cewa shi ne Kakakin Yaɗa Labarai na Shugaba Buhari ya na damfarar mutane ‘yan ƙasar waje kuɗaɗe.

Mai Shari’a ya umarci EFCC ta ƙwace kadarorin da mutumin ya mallaka, su koma mallakin Gwamnatin Tarayya.

Sannan kuma an umarce shi ya biya wanda ya damfara ɗin dukkan kuɗaɗen sa.