BINCIKEN ‘Pandora Papers’: Yadda Fasto David Oyedepo ya kafa kamfanin karkatar da mahaukatan kuɗaɗe a ƙasar waje

Bayan Fasto Chris Oyakhilome na Cocin Chris Embassy da T.B Joshua na Cocin SCOAN, a yanzu kuma an bankaɗo cewa Babban Faston Living Faith David Oyedepo ya shiga sahun na uku a jerin fastocin Najeriya waɗanda su ka kafa kamfani da ƙasar waje ana karkatar da mahaukatan kuɗaɗe a Tsibirin Virgin Islands.

Binciken Fallasa da ke kan yi mai suna Pandora Papers ne ya bankaɗo cewa David Oyedepo ya kasance ya maida hankali wajen tara abin duniya ya na kimshewa a ƙasashen waje, a lokacin da a nan cikin Najeriya ya ke yi wa miliyoyin mabiyan sa wa’azin gudun duniya.

Fasto Oyedepo: Mai Neman Lahira Ya Ɓuge Gina Aljannar Duniya:

Cikin 2007 Oyedepo ya tuntuɓi wasu dillalan gada-gada a Landan da ake kira Business Centrum Limited, domin su yi masa aikin kafa kamfanin da zai riƙa amfani da shi ya na ɓoye kuɗaɗe a Tsibirin British Virgin Islands, domin shi da iyalan sa.

Samun kwangilar wannan aikin gada-gada ke da wuya, sai Business Centrum Limited ya tuntuɓi wani kamfanin taya ‘yan harƙalla shirya gidoga na
Trident Trust Group. Shi kuma wannan kamfani ya shahara a duniya wajen ɓoye sirrin duk wata harƙallar da aka ba shi riƙon amana.

Daga nan an Oyedepo da taimakon waɗannan ‘yan daƙa-daƙa, ya kafa kamfani mai suna Zadok Investments Limited a cikin watan Agusta, 2007.

An danƙara hannayen jari 50,000, kowace a kan darajar dala 1.

Duk da cewa kamfanin Zadok Investments Limited Daraktoci uku gare shi, wato Oyedepo da ‘ya’yan su biyu, David (Junior) da Isaac, duk wasu sauran dangin Oyedepo an tsarma sunayen su a matsayin masu hannayen jari a cikin sunayen masu hannayen jari a cikin kamfanin.

David da matar sa Faith su ke da kashi 30 cikin 100 na hannayen jarin.

David (Junior) wanda a cikin 2016 aka naɗa shi Fasto mai kula da ‘Faith Tabanacle’ ke da kashi 10 cikin 100. Sai Isaac, wanda shi ne shugaban reshen cocin da ke Maryland, Amurka, shi ma ya na da kashi 10 bisa 100.

Sai wasu ‘ya’yan Oyedepo su biyu, Love da Joy, waɗanda ke da kashi 10 bisa 100 kowanen su.

A takardun bayanan kamfanin ba a rattaba irin hada-hadar cinikayyar da zai yi ko ya riƙa yi ba.

Sai dai a fakaice wani rami ne aka gina kawai domin kimshe maƙudan kuɗaɗen da ake kwasa daga Najeriya ana turawa ƙasashen waje.

PREMIUM TIMES ta tuntuɓi Oyedepo ta lambar wayar sa, amma bai amsa tambayoyin da aka yi aika masa ta hanyar saƙon tes.

Oyedepo ya samo sunan kamfanin sa daga sunan almajirin Annabi Dawuda mai suna Zadok. Kuma ya kasance ya na da biyayya sosai.

Cikin 2011 Mujallar Forbes ta buga cewa Fasto Oyedepo ya mallaki dala miliyan 150. Abin ya bai wa Oyedepo haushi.

Watannin baya Oyedepo ya kori wasu fastoci da ke aiki a ƙarƙashin cocin sa, ba tare da biyan su haƙƙoƙin su ba.

Oyedepo ke da Jami’o’in da su ka fi tsadar karatu a Najeriya, Covenant University. Kuma shi ke da Landmark University a garin Omu-Aran, Jihar Kwara.

Kuma ya na da makarantun firamare da kuma na sakandare na kwana.

Oyedepo ya mallaki jiragen shiga na hawa ba na haya ba, guda huɗu. Gufstream V kaɗai dala miliyan 30 ya saye shi.

Fasto Oyedepo ke da kamfanin Hebron Oil da sauran hada-hadar da ya ke yi daban-daban.