Zan samar wa duk wani dan Najeriya tsaro daga ‘yan bindiga da mahara a duk inda yake – Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi alwashin samar wa ‘yan Najeriya tsaro a duk inda suka a fadin kasar nan.

Buhari ya bayyana haka a jawabin da yayi a wajen yaye daliban makarantar koyon aikin Soja, NDA a Kaduna.

Buhari wanda ya halarci taron da kansa ya ce abinda gwamnatin sa ta fi maida hankali a akai yanzu shine samar da tsaro ga ‘yan Najeriya.

” Ina muku fatan Alkahiri ga dukkan daliban da ake yayewa a yau, sai dai kuma ba kamar yadda wadanda suka gama karfatu a baya ba, ku zo ne a lokacin da kasarnan ke cikin halin rashin tsaro da wasu matsalolin da ya addabi mutane. Saboda haka za ku fuskanci kalubale.

Buhari ya kara da cewa gwamnatin sa ta siyo manyan kayan aiki daga kasashen waje. Wadannan kayan aiki za a yi amfani dasu wajen ragargaza yan ta’adda, mahara da duk wanda ya shiga wa kasa gaba don tada zaune tsaye.

A karshe ya ya yabawa shugaban makarantar, Ibrahim Yusuf kan yadda ya gyara da kawata ta ta yadda ko ina a duniya ana alfahari da ita.

Buhari ya isa garin Kaduna tun ranar Juma’a. Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya tare da manyan jami’an gwamnati a jihar suka tarbe shi a filin jirgin saman Kaduna.