AREWA A HANNUN ‘YAN BINDIGA: Kwanaki 30 bayan garkuwa da Sarkin Bunguɗu, an biya kuɗin fansa amma har yau babu labarin sa

Har yau iyalai, abokai da fadawan Sarkin Bunguɗu, Hassan Attahiru ba su san halin da ya ke ciki ba, kwanaki 30 bayan kama shi da yin garkuwa da shi.

‘Yan bindiga sun kama shi a kan hanyar Abuja daga Kaduna, inda bayan sun bindige ɗan sandan da ke kare lafiyar sa, sun kuma haɗa da wani ɗan sanda ɗaya tare da Sarkin, duk su ka nausa cikin daji da su.

Lamarin ya faru a ranar 14 Ga Satumba, wanda tun bayan nan ba a sake jin ɗuriyar sa ba.

Sarkin Bunguɗu wanda ake wa lakabi na Sarautar Sarkin Fulanin Bunguɗu, tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa ne.

Sakataren Masarautar Bunguɗu Muhammadu Usman, ya shaida wa BBC Hausa cewa a baya dai wasu makusantan Sarki da ke wajen Zamfara sun riƙa magana da masu garkuwar, inda su ka yi ƙoƙarin karɓo shi.

Ya ce amma saboda matsalar kulle layukan waya, a yanzu ba su da labarin halin da Sarkin ya ke ciki.

Wata majiya a Fadar Sarkin Bunguɗu da ba ta so PREMIUM TIMES ta ambaci sunan ta, ta ce “yanzu haka ba mu san halin da ya ke ciki ba. Ko ya na da rai, ko babu. Amma dai mu na da yaƙini a ran mu cewa ya na da rai.

“A baya an tattauna, har an kai kuɗin fansa. Amma kuma daga nan ba mu ƙara jin wani bayani ba, ko muryar sa ba a sake ji ba. Bayan kuma sun ce za su sake shi.”

Idan ba a manta ba, ranar 15 Ga Maris, an yi garkuwa da Sarkin Bukkuyum shi ma na Jihar Zamfara, bayan an yi musayar wuta da jami’an tsaron sa.

Sai dai kuma an sake shi bayan sati ɗaya da kama shi.