Marigayi Alhaji Bashir Othman Tofa: Abinda Na Sani Game Da Rayuwarsa, Daga Muhammad Bashir

A al’adar Dan Adam, mutuwa ko rashi ‘kullum’ ta fi bayar da mamaki akan haihuwa ko samun ƙaruwa – sabida kewar da take sanyawa aji, sakamakon shaƙuwa da wanda ya rasu. Sai dai irin mamakin da mutuwa ke sanyawa mutum a cikin zuciyar sa, yana tattare ne da razani, da tsoro, da jimami da kuma bacin rai.

To amma sabida tasirin da Musulunci yake dashi a zukatan mu, duk wadannan ‘ƙarshe’ daina jin su muke yi; mu dawo muna godewa Allah sabida abinda ya dauka/kwace daga gare mu, da ma ‘can’ MallakinSa ne.

Tashi da labarin rasuwar Alhaji Bashir Othman Tofa a yau Litinin 3 ga watan Janairun shekarar 2022, ya girgiza ni gaskiya. Sabida na san shi; ya san ni. Cikin haduwa ta dashi ta ƙasa da shekaru biyu ko uku ‘kacal’ na koyi sabbin dabi’u da halaye masu kyau a wurin sa.

Dama can, Marigayi Alhaji Bashir Othman Tofa, mutum ne mai yawan kawo mutuwa a lissafin sa, domin yana da matuƙar wahala ka zauna dashi (zama na tattaunawa akan batutuwan rayuwa) baka ji ya yi maka maganar mutuwa ba…har yakan fadin cewa “ko wannan gidan da nake ciki, wata rana dole zan tafi; na bar shi…na barwa magada.”

Mutum ne mai kishin al’uma (musamman ‘yan Arewa da kuma jama’ar Kano); ga shi da zurfin tunani da sanin makamar rayuwa da iya zama da jama’a. Bashir Tofa, Dattijo ne mai son kiyaye lokaci da kuma alƙawari – kuma yana son ciyarwa, musamman idan kaje gidansa.

Mutum ne wanda duk lokacin da aka kusance shi, yana bayar da sha’awa sabida yana da tsari mai kyau – ga son yin Ibada da kuma fara’a. Haka nan, Alhaji Bashir Othman Tofa yana bakin-cikin halin da wadansu shugabanni suka jefa al’uma a ciki na ƙangin talauci da matsi, wannan tasa kullum burinsa shine “yaya za’a taimakawa mutane” ko da kuwa ta hanyar wayar da kan mutanen ko wacce anguwa ne, domin su tashi tsaye wajen tallafawa mutanen su ne.

Sa’annan, ba bu wata ƙungiya mai kyakkyawar manufa da za ta tunkare shi, face ya ba ta lokaci isashshe; ya ba ta shawarwari da kuma kalaman ƙara ƙwarin gwiwa da kuma alwashin tallafa masu a duk lokacin da buƙatar hakan ta taso – domin amfanin al’uma.

Mutum ne mai kiyaye shiga duk abinda bai shafe shi ba – ba shi da katsalandan ko shish-shigi a lamuran mutane – sai idan an zalunce su ne. Lallai, wadannan sune kadan daga cikin halayensa, dana iya kiyaye wa.

Rashin Alhaji Bashir Othman Tofa, babban rashi ne ga ilahirin al’umar jihar Kano, dana Arewa dama jama’ar Najeriya baki daya. Ina miƙa sakon ta’aziyya ta ga duk Musulmi da musamman H.E Engr Bashir I. Bashir. Allah Yasa Mu Gama Lafiya!