Barcelona Ta Maida Martani Akan Zargin Da Ake Mata
Kungiyar kwallon kafar Barcelona ta kasar Spain ta maida martani kan binciken da ake yi kan ta, bisa tuhumar biyan alkalan wasa don ba su nasara, tana mai bayyana zargin a zaman farmaki kawai na adawa.