RIKICIN BAUCHI: Yadda hasalallun matasa suka cinna wa gidaje sama da 60, babura uku wuta sannan suka kashe wani dattijo

Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta bayyana cewa wasu matasa sun kashe mutum daya, sun Kona gidaje 64 da babura 3 na miliyoyin kudade a rikicin karamar hukumar Bogoro.
Kakakin rundunar SP Ahmed Wakil ya sanar da haka wa manema labarai a garin Bauchi ranar Lahadi.
Wakil ya ce hakan ya auku ne a dalilin zanga-zanga da matasan suka yi a kauyen Sang
“A ranar 15 ga Afrilun 2023 da misalin karfe 7 na yamma rundunar ‘yan sanda ta samu labarin rikicin da ya barke a karamar hukumar Bogoro.
“Sakamakon binciken da rundunar ta gudanar ya nuna cewa rikicin ya somo ne daga kauyen Sang dake karamar hukumar Bogoro yayin da ake nada sarkin Sang.
“Yayin da ake nada sarkin ne wasu matasa suka yi kan mi uwa dawabi da har aka kashe mutum daya, suka cinna wa gidaje 64 da babura uku.
“A dalilin rikicin Wani Spollos Danlami mai shekara 70 ya rasa ran sa sannan Wani Naemiya Bature mai shekara 65 da wasu mutane sun ji rauni.
Zuwa yanzu zaman lafiya ya dawo kauyen.
Kakakin ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar Aminu Alhassan ya bada umurin gudanar da bincike domin kamo mutanen da suke tada wannan rikici a wuri naɗin sabon sarkin Sang din.