BARAZANAR ‘EMI LOKAN’ 2023: Ganganci da kasassaɓa ce idan aka zaɓi wanda ya yi wa ‘yan Najeriya ‘a ba ni a huta’ – Obasanjo kan Tinubu

Tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo, ya bayyana cewa babban kuskure ne ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Bola Tinubu ya tafka, lokacin da ya yi wa Shugaba Muhammadu Buhari barazanar cewa yanzu lokacin sa ne, don haka a ba shi mulki a huta.
Tinubu dai ya yi wannan barazana ne lokacin da ya ke kamfen ɗin takarar shugabancin ƙasa kafin zaɓen fidda gwani, a Gidan Gwamnatin Jihar Ogun.
Wannan barazana wadda ya yi a cikin harshen Yarabanci, wato ’emi lokan’, wadda ta ke nufi lokaci na ne, Tinubu ya yi caccakar ce ga Shugaba Muhammadu Buhari, wanda a cikin kakkausan kalaman na sa, har ya riƙa yi wa Buhari gorin yadda ya taimake shi ya zama shugaban ƙasa, kuma kafin shi ya ce ya goyi bayan Atiku Abubakar da Nuhu Ribadu a baya.
Sai dai kuma a cikin wasiƙar da Obasanjo ya fitar a ranar Lahadi, ya ce “furucin lokaci ne ne yanzu ba ni a huta da Tinubu ya yi, babban kuskure ne ga shugabancin Najeriya a yanzu.”
“Don haka ba za a iya bunƙasa ƙasa ta zama ƙasaitacciya a ƙarƙashin wanda ya yi irin wannan barazana ba, balle har a samu nagartar zamantakewa tsakanin ‘yan Najeriya su ya su.”
Daga nan Obasanjo ya ƙara da cewa babu wani ɗan Najeriya da zai iya fitowa ya bugi ƙirji cewa shi ne ke da maganin da warkar wa Najeriya ciwon da ke damun ta.
“Don haka kamata ya yi Tinubu ya yi amfani da kalmar ‘mu’ ba ‘ni’ ba.” Inji Obasanjo.
Buhari Ya Maida Najeriya Baya, Fiye Da Taɓarɓarewar Ta Kafin 1999 – Obasanjo:
Da ya ke magana kan mulkin Buhari wanda zai ƙare nan da watanni biyar bayan cikar wa’adin zango biyu na shekaru takwas, Obasanjo ya ce wannan gwamnatin ta maida Najeriya baya, ta yi taɓarɓarewar da ta fi kafin 1999 muni.
“Ina matuƙar damuwa ganin yadda masu takarar shugabancin ƙasa a yanzu sun kasa fahimtar irin yadda mulkin Buhari ya maida Najeriya baya, taɓarɓarewar ma har ta fi yadda ƙasar nan ta ke kafin 1999 muni, lokacin da na karɓi mulki a hannun sojoji.”