Kotu ta bada belin mutumin da ya lakaɗawa ɗan sanda duka kan naira 150,000

Kotun majistare dake Ile-Ife jihar Osun ta bada belin Sunday Awominure mai shekara 22 kan naira 150,000 bayan an same shi da laifin lakadawa wani dan sanda dukan tsiya da ji masa rauni.
Alkalin kotun A. O. Famuyide ya ce Sunday zai gabatar da shaida daya sannan ya tabbatar cewa shaidan da zai gabatar na da wurin zama, aikin yi tare da hotunan sa guda biyu domin gabatar wa kotu.
Famuyide ya ce za ci gaba da shari’a ranar 19 ga Janairu 2023.
Bayan haka dan sandan da ya shigar da karar Emmanuel Abdullahi ya bayyana cewa Sunday ya lakadawa dan sandan dukan tsiya ranar 21 ga Disambar 2022 da misalin karfe 1:10 na dare a lamba 3 layin Otutu dake Ile-Ife.
Abdullahi ya ce a wannan rana Sunday ya fara lakadawa wani Odedoyin Ayobami dukan tsiya inda har ya ji masa rauni a goshi da hanayen sa biyu.
Ya ce hakan ya faru bayan Sunday ya tada rikici a wurin da mutane ke shakatawa dake Otutu a Ile-Ife.
Abdullahi ya ce dalilin haka ne Kaftin Abah Johnson ya kawo dauki inda garin haka ne Sunday ya haɗa da shi ya yi musu dukan tsiya.
“Sunday ya rika naushin ɗan sandan har sai da yayi masa ruɗuruɗu da fuska, ya yayyaga masa rigar sa na ɗan sanda, ya tsinka masa agogo sannan kuɗin sa naira 15,000 suka bace.
Ya ce rundunar ta kama Sunday bisa laifukan da suka hada da haɗin baki, yi wa dan sanda duka, tada hankalin mutane da lalata kayan gwamnati.
Sunday dai ya musanta aikata duk laifukan da kotun zarginsa da su.