NDLEA ta kama mata 127 cikin ƴan kwaya 1,078 da hukumar ta kama a jihar Kano a 2022

Hukumar hana Sha da safarar muggan kwayoyi ta kasa NDLEA reshen jihar Kano ta bayyana cewa ta kama ton 9 na muggan kwayoyi da kudinsu ya kai naira biliyan 1.5 sannan ta kama masu sha da safarar muggan kwayoyi mutum 1,078 a cikin watanni 12 a jihar.
Shugaban hukumar Abubakar Idris-Ahmad ya sanar da haka ranar a cikin makon jiya a garin Kano.
Ya ce hukumar ta Kai samame wurare 82 da suka yi kaurin suna wajen sha da safarar muggan kwayoyi a ciki da wajen jihar.
“A dalilin haka muka kama mutum 1,078 dake da alaka da Sha ko safaran haramtattun kwayoyi inda a ciki akwai mata 127 da maza 951.
“Mun Kuma kama kilogram 8,386.733 na haramtattun kwayoyi da a ciki akwai kilogram 6,607.492 na ganyen wiwi, kilogram 1,778.388 na wasu haramtattun kwayoyi, gram 451 na hodar ibilis, gram 125 na hodar ibilis da gram 277 na methamphetamine.
Idris-Ahmad ya ce kotu ta yanke wa mutum 113 daga cikin yawan da ta kama hukunci, ta kona gonakin wiwi biyar sannan ta na kula da mutum sama da 1,844 dake fama da matsalolin tabuwar hankali a dalilin ta’ammali da kwayoyi.
“Hukumar ta wayar da kan dalibai kan sanin illar safara da ta’ammali da muggan kwayoyi a makarantun boko 150, ta yi wa sarakunan gargajiya 141 gwajin kwayoyi da yi wa mutum 164 gwajin kafin a lokacin neman bizar fita kasar waje.
Idris-Ahmad ya kara da cewa Shugaban hukumar Buba Marwa ya amince a gina sabbin ofisoshi biyu a jihar domin ci gaba da ayyukan hukumar.
“Muna mika godiya ga sauran hukumomin tsaro, kungiyoyin dake zaman kansu, shugabanin gargajiya da gidajen jaridu wajen wayar da kan mutane illar sha ko safarar muggan kwayoyi.
Idris-Ahmad ya yi kira ga gwamnati da masu ruwa da tsaki a jihar da su ci gaba da hada hannu da hukumar domin samun nasarar akan aikin da ake yi.