‘Bani da ɗan da ya yi girman tsayawa takarar shugaban kasa’ – Tinubu ga Osinbajo

Tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Tinubu ya bayyana cewa bashi da ɗan da ya kai matsayin bayyana kansa ɗan takarar shugaban kasa a Najeriya.
Wannan shine ne amsar da Tinubu ya baiwa ƴan jarida da suka tambaye shi me zai ce game da fitowa takarar shugaban kasa da mataimakin shugaban kasa yayi yau Litinin.
“Me za ka ce gane da fitowa takara da ‘Ɗan ka’ Yemi Osinbajo ya yi? ” Bani da ɗa da ya isa fitowa takarar shugaban kasa.
Tinubu ya yi ganawa ta musamman da wasu daga cikin gwamnonin jam’iyyar APC a gidan gwamnan Kebbi a Abuja.
Wannan ganawa na da nasaba ne da cigaba da tattaunawa da Tinubun yake yi da ƴaƴan Jam’iyyar APC kan takararar shugabancin kasar nan da yake da burin yi.
Sai dai kuma kamar yadda aka sani, a safiyar Litinin ɗin yau, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya bayyana aniyarsa na yin takarar shugaban kasa a 2023.
Wannan abu ya jawo cecekuce a shafukan sada zumunta inda wasu da dama ke ganin cin amana ne Osinbajo yayi na fitowa takara a daidai Tinubu wanda shine ya goya shi a siyasance har ya kai inda yake a yanzu a siyasa.
Masu yun sharhi na ganin cewa tunda Tinubu ya nuna aniyarsa na yin takarar shugaban ƙasa, bai kamata a ce Osinbajo ya fito takara ba kwata-kwata. Maimakon haka sai dai ya mara wa Tinubun baya hakarsa ya cimma ruwa.