BAJEKOLIN ƁARAYIN GWAMNATI DA MAZAMBATA: EFCC ta ƙwato naira biliyan 152, dala miliyan 386 kuma ta maka mutum 2,220 kotu cikin 2021

Hukumar EFCC ta bayyana cewa tsakanin Janairu zuwa Disamba, 2021, ta samu nasarar ƙwato zunzurutun naira biliyan 152 da kuma dala miliyan 386 cikin shekarar 2021.

Cikin Wata sanarwa da Kakakin Yaɗa Labaran EFCC, Wilson Uwujaren ne ya sanar da haka a cikin wata sanarwar da ya aika wa manema labarai a ranar Litinin a Abuja.

Uwujaren ya ci gaba da cewa banda maƙudan kuɗaɗen da aka ƙwato, EFCC ta maka mutum 2,220 kotu a cikin 2021 a kan laifuka daban-daban da suka shafi wawurar kuɗaɗen gwamnati da zamba-cikin aminci da kuma damfara.

Shugaban EFCC Abdulrashid Bawa, ya ce yawancin kuɗaɗen da EFCC ta ƙwato ɗin mallakar Gwamnatin Tarayya ne. Amma akwai na jihohi da na ƙananan hukumomi.

“Kuma akwai kuɗaɗen kamfanoni da kuɗaɗen ɗaiɗaikun mutanen da aka zambata ko aka damfara.” Bawa ya ce duk an ƙwato masu kuɗaɗen na su.

EFCC ta ce tun da aka kafa hukumar ba ta taɓa gurfanar da mutane masu yawa a kotu ba, kamar cikin 2021.

Bawa ya gode wa dukkan jami’an EFCC bisa irin jajircewar da su ke nunawa da kuma aiki tuƙuru.