2023: Wa ya kamata ya zama gwamnan Jigawa? Daga Ahmed Ilallah

Jigawa wacce take da alúmmah sama da miliyan biyar wanda akasari wannan alúmmah suna zaune ne a karkara, wanda a ka kirkirota sama da shekaru talatin daga tsohuwar jihar Kano, kusan dukkanin kananan hukumomin da suka zamanto a jihar jigawa, sune mafi koma baya a harkar ci gaba ta fannoni daban daban, kama daga ilimi, kiwon lafiya da ma abubuwan more rayuwa, amma fa har yanzu fa akwai wadannan matsalolin a bangare da dama na wannan jahar.

Duk da kasancewar jahar ta samu chanji da cigaba a fannoni da dama, kama daga siyasa da sauran fannoni na cigaba, amma fa har yanzu akwai matsala ta tattalin arziki, koma bayan ilimi, lafiya da mafi muhimman ci cigaban siyasa, ta yadda za ta bawa kowa da kowa damar a damula da shi wajen shugabanci da bada gudunmawa sa don raya jahar.

Siyasa a jihar jigawa da yadda ake aiwatar da ita ta babbanta da sauran jahohin arewacin Nijeriya, duk da kasancewar ta kafa tarihi wajen wadanda suka zamanto gwamnonin jahar, gwamnoninta na farko matasa ne a lokacin da aka zabe su, Barrister Ali Saád da Saminu Turaki, wanda duka sun zamanto gwamnoni suna kasa da shekaru 40, sannnan Gov. Sule Lamido da Gov. Badaru Abubakar wanda a ka zabe su a matakin dattijai, kuma kowa ya yi bakin kokarin sa wajen kawo cigaban jihar jigawa, kuma dukkanin jamaíyyun kasar nan ANPP, PDP, APC sun mulki Jigawa.

Siyasar yanki da bangaranci tana yin tasiri a jigawa, musamman lokacin da aka zo zabe, yan siyasa ko masu neman mulki kanyi amafani da siyasar masarauta don damulawa alúmma tunani da cusa musu siyasar kabilanci don biyan bukatar kansu, yayin da ake mancewa matsaloli da bukatar jihar a gefe. Ta wani gefen a mance da chanchanta, amana da ilimin wanda ya kamata ya shugabance mu, dama hana alúmmah suyi zabe bisa chanchanta. Karancin yawan yan siyasa, musamman rashin fittattun yan boko da yan kasuwa da muhimman mutane cikin alúmma shiga harkokin siyasa ya bar jagorancin siyasar da ma mulkin a hannu tsiraren mutane, wanda hakan ya sanya a wani lokutan dimokaradiyyar bata banbanta da mulukiyya, nadawa mutane ake shugabannin su maimakon a bada damar a yi dimokaradiyya ta hanyar gamsassiyar takara da zabe.

In aka yi bibiya akan cigaban da Jigawa ta samu a shekara ashirin baya, akwai tsari da cigaba da kowane gwamna ya bayar wajen kawo chanji da ci gaba a jigawa, tsohon gwamna Saminu Turaki a cikin kaddan daga cikin chanjin da ya kawo ya hada da bunkasa ilimin farko, kawo tsarin 9-3 na karatun basic schools a jigawa, ya kawo tsari da bunkasa ilimin sadarwa na zamani (ICT) ta yadda ya samar da kamfanin galaxy wanda a zamanin sa Jigawa tayi fice akan ilimin ICT da ma amfani da kafofin sadarwa na zamani, tsarin na yakar talauchi na Millennium Village ya kawo cigaba kwarai wajen bunkasa arzikin jigawa, ya kirkiri sabbin hanyoyi mota don hada garuruwan jihar kamar sabuwar hanyar dutse zuwa kazaure, daga Maigatari zuwa Birniwa (Western Bye-Pass) da sauransu.

Tsohon Gwamna Sule Lamido a zamanin sa yayi kokarin maida jahar Jigawa, jahar Birni da gina Babban Birnin Jahar don yayi kafada da sauran manyan birane a Nijeriya, ya samar wa da Jahar Tashar Jirgin Sama (Airport), ya samar da filayen taro da dakunan taro na zamani, kamar Aminu Kano Triangle, MDI, Sir Ahmadu Bello Hall da sauran su, ya kammala babbar sakatariyar jaha, ya chanja fasalin gidan gwamnati da majalissar jaha, gwamna sule lamido ya bunkasa ilimi musamma manyan makarantu na gaba da sakandare, shi ya kirkiro Jamiár farko mallakar jahar a garin Kafin Hausa.

Gwamna Mohammad Badaru Abubakar wanda yake zango na karshe a kan mulkin jahar jigawa, yana nasa kokarin musamman wajen samar da hanoyin mota, wanda zuwa wannan lokacin ya gina sama da kilomita dubu a fadin jahar jigawa, an gina tagwayen hanyoyi a wasu manyan biranen jahar. A bangaren ilimi ya gina manyan makarantun sikandare guda 27 don rage cinkoson dalibai da daruruwan kananan makarantun sikandare a fadin jahar, ya daga likkafar makarantar College na Hadjia da Ringim zuwa Polytechnic da College of Education, a harkar lafiya ya bunkasa tsarin Primary Healthcare System, an gyara da ginawa kananan asibitoci a kowace mazaba ta jahar, an samar babbar asibibiti a kowace hedikwatar karamar hukuma, ya kawo chanji da zamanatar da bunkasa harkar noma a fadin jahar jigawa, a yau jahar tayi fice wajen noman ridi, shinkafa, alkama, zoborodo da sauran su.

Amma fa har yanzu akwai sauran rina a kaba, duk da aiyukan da wadannan gwamnoni suka yi a kalubale masu tarun yawa da har yanzu suke addabar alúmmar jihar jigawa, musamman ma haddikan alúmomin jahar da fahimtar juna, matsalar bangaren ilimi, lafiya, tattalin arziki da kuma yaki da talauchin da yak e addabar mutanen jahar. Har yanzu Jigawa na cikin jahohi da suke koma baya a cigaban ilimi, lafiya.Kadan daga kalubalen jigawa a harkar lafiya ya hada yawan mutuwar mata a wajen haihuwa, yawan mutuwar kananan yara, gaza yakar cututtukan da ke kashe alúmman irin su malaria, ciwon koda da sauran cutukan da za a iya shawo kan su. Harkar lafiya a jihar jigawa tana da matsalar kwararru da isassun likitoci da maáikatan jinya a fadin jahar.

A bangaren ilimi akwai kaluballe masu yawa da suka hada matsalar ilimin mata, matsalar malamai da duk kusan makarantun jahar jigawa daga primary schools har manyan makarantu. A bangaren makarantun sakandare akwai kalubale na rashin dakunan koyon kimiya wato laboratory a kusan yawancin manyan makarantun wannan jahar. Dadi da kari fa har yanzu jigawa bata iya samar da kashi goma wato 10% na kasafin kudinta na shekara da ga harajin da take samu na cikin gida ba.

To komi ma a ke ciki, lokaci yayi bisa nazartar cigaban da aka samu a baya da kuma wuraren da a ka gaza kaiwa ta yadda za a samar da cigaba mai dorewa.

Dukkanin masu ruwa da tsaki ya kamata suyi tunanin matsalolin Jigawa a yau da tunan nin yadda za a magance su. Ya zama wajibi a yau a bijiro da taswirar da a ke bukata Jigawa ta kai na karami, matsakaici, dogon lokaci da hanyoyin da za a cimma su.

Saboda haka, a irin wannan zamani, duka mai son zama gwamna ya kamata ya kasance mai ilimin jihar jigawa da yankunnanta, kauyukanta da al’umomin ta, ya kasance mai ilimi da gogewa ta zamani, kuma dan siyasa, kwararre wajen iya diplomasiyya, kwararre wajen magance matsalolin alúmma na yau kullum, wanda yake da hikimar bunkasa tattalin arzikin da jigawa ta ke da shi na fannin maádinai, noma da fasaha.

Abu mafi muhimmanci, ya zamanto dan Jahar Jigawa, mai kishin Jihar Jigawa, ya zama wakilin jigawa ba wakilin gari, yanki ko masaurata ba.

[email protected]