Babu laifin da na aikata, fim ne na yi kuma ba na batsa ko fasikanci bane – Inji Furodusan fim din ‘Makaranta’ Mukhtar

Hukumar tantance fina-finai ta jihar Kano ta sanar cewa ta na neman wanda ya shirya fim ɗin nan da ya jawo cecekuce mai suna Makaranta, wato Aminu Mukhtar ruwa a jallo.

Hukumar ta ce ta na neman wanda ya shirya fim ɗinne saboda karya dokar shirya finafinai ta hukumar sa yayi a lokacin da ya shirya wannan fim ɗin, cewa kusan duka abinda ya nuna a cikin shirin ya saɓa wa al’adu da addinin musulunci.

A tattaunawar da ya yi da BBC Pidgin shugaban hukumar Ismail Afakallah ya ce hukumar ta gayyaci Mukhtar domin ya yi bayani kan dalilan da ya sa ya shirya irin wannan fim.

“Hukumar ta gayyaci Mukhtar kan wannan fim na batsa da ya yi da yadda ya saki fim din ba tare da izinin hukumar ba sannan ko tallar fim din da ya saki ba samu amincewar hukumar ba.

Shi kuwa Mukhtar ya ce fim din da ya yi ba na batsa bane ko fasiƙanci kamar yadda hukumar take zargi.

Ya ce tabas fin din da Hausa aka yi amma akwai harsunan sama da 17 da aka yi amfani da su a fim din sannan ba a jihar Kano aka yi fim din ba.

“Saboda haka ban ga dalilin da zai sa hukumar tada jijiyoyin wuya akan fim ɗin ba.

“Fim din da na yi ba a kan jima’i bane kawai, fim din ya taɓo matsalar yi wa mata kaciya da sauran matsalolin da mata ke fuskanta musamman a makarantun mu.

Ra’ayoyin mutane

A gajeruwar tallar fim din da PREMIUM TIMES HAUSA ta gani a yanar gizo an ga yadda wasu daliban makarantar ke rawa a wani casu da aka yi a makarantar inda wasu a cikinsu ke magana akan akan jima’i da kalle-kallen nonuwan juna.

A tattaunawa da ya yi da PREMIUM TIMES HAUSA wani mai shirya fina-finan Hausa kuma mazaunin garin Kaduna Isah Abdu ya ce lalle abin da Mukhtar ya yi bai dace ba.

“Ban ga fim din ba tallar kawai na kalla kuma a matsayina na mai shirya fim a Arewa bai kamata ya yi fim irin haka ba saboda a gani na batsa yayi yawa a ciki.

“Tun daga kalaman da aka yi amfani da su kaya da botsarewar da ‘yan mata kanana suka yi a cikin fim ɗin duk lalata tarbiya ne. Wai wata fa har nonon kawarta ta ke leƙawa don don shegantaka.

Shahararriyar mai yin sharhi akan finafinan Kannywood, Hassana Ɗalhat ta bayyana mana cewa
ita ma bata goyi bayan yadda aka shirya fim irin haka ba cewa a kwai gyara.

“Mukhtar ya ce ba a Kano ya yi fim din ba amma ai da Hausa aka yi sannan mutane za su gani kuma su yi koyi da abinda suka gani.

Mutum sama da 61,000 ne suka kalli tallan fim din Makaranta na Mukhtar a shafin YouTube sannan kuma an yi amfani da harsunan yarbanci da Turanci.