Zan siyar da kwanon da na rufe saman gidana in biya kuɗin fansar Ɗa na dake tsare hannun ƴan bindiga – Dattijo Sa’idu Faskari

Malam Sa’idu Faskari wani dattijo kuma mazaunin garin Faskari dake jihar Katsina.

Sa’idu ya shafe kwanaki 13 tsare hannun ƴan bindiga da suka yi garkuwa da shi.

Dakyar suka amince aka aika musu da naira 50,000 su saki dattijon. Sai dai kuma rashin rabo, ɗan malam Sa’idu da ya kai wa ƴan bindiga kuɗin fansan, sai suka tsare shi shima wai sai an kai musu naira 100,000 Kuɗin fansa kafin su saki ɗan.

Maharan sai suka saki dattijon suka riƙe ɗan.

Wakilin jaridar Katsina Daily Post, Ibrahim Bawa ne yayi tattaki har gidan Malam Sa’idu a garin Faskari domin yin ido hudu da shi.

Ko da Bawa ya isa gidan dattijo Sa’idu ya iske shi tare da ma’aikata ana cire rufin saman gidan sa zai je ya saida ya aika wa ma’aikatan kuɗin fansar ɗan sa daga hannun ƴan bindiga.