Akalla mutum 6 ne suka jikkata a rikin fulani makiyaya da manoma a Jigawa

Kwamishinan Ƴan sandan jihar Jigawa Aliyu Tafida ya bayyana cewa mutum shida sun ji rauni kuma mutum daya ya rasa ransa a rikicin makiyaya da manoma da aka yi a karamar hukumar Kirikasamma.

Tafida wanda ya sanar da haka ranar Juma’a ya ce rikicin ya auku ne tun a ranar Talatar makon jiya.

Ya ce bayan ya ziyarci karamar hukumar ya aika ma’aikata domin samar da zaman lafiya a yankin.

Tafida ya ce rundunar ta gano cewa makiyaya sun kashe wani manomi mai suna Buhari Haladu a rikicin.

Wani mazaunin karamar hukumar Idris Madaci ya bayyana wa wakilin PREMIUM TIMES cewa makiyayan ne suka fara kai wa manoman hari.

“Makiyayan sun yi amfani da sanduna, dadduna da mashi wajen kai wa manoman hari.

Madaci ya ce makiyayan sun kashe Haladu inda suka sare Kan sa, hannayen sa da wasu sassan jikinsa.

Ya ce suna zargin cewa makiyayan da suka far wa manoman baki ne daga jihohin da suke makwabtaka da su da Jamhuruyyar Neja.

Wannan rikicin ya faru bayan wata daya da aka yi rikici irin haka ya faru a karamar hukumar.

Mazauna jihar Jigawa sun yi korafin kan yadda gwamnati ta ƙasa sassanta rikicin da aka Yi shekaru da dama ana fama da shi a tsakanin makiyaya da manoma a yankin.