Babu hujjar cewa Boko Haram ta sanya dokar shari’a a jihar Neja – Binciken DUBAWA

Zargi- Boko Harama ta sanya dokar shari’a a jihar Neja

A Najeriya jihohi 12 wadanda kuma ke da rinjaye a yawan al’ummar musulmi na amfani da dokokin shari’a tun shekarar 1999 lokacin da gwamnan jihar Zamfara na wancan lokacin Ahmad Sani Yerima ya kirkiro shari’ar musulunci a jihar.

An aiyana amfani da cikakkun dokokin sharia a jihohi 12 a wannan shekarar kuma jihohin su da kansu a wancan lokaci sun kirkiro hukumomi da zai rika kula da ayyukan, dabi’u da yadda mutane za su rika gudanar da al’amurorin su da suka hada da hukumomin kula da yadda za a rika tarawa da raba zakka da na hisbah, wacce za ta zama duba gari wajen tabbatar da an bi dokokin musulunci a jihar.

Wani mai amfani da shafin tiwita wanda ke da ma’abota 269,000 mai suna Adetutu Balogun da shafin @Tutsy22 ranar 7 ga watan Oktoba 2021 ya wallafa wani zargi a shafin sa cewa Boko Haram ta kafa dokar shari’a ga wasu mazauna garuruwa dake karamar hukumar Shiroro a jihar Neja. Sannan kuma wai sun sanar cewa duk musulmi da kiristocin dake zama a wadannan yankuna za su aurar da duk macen da ta kai shekara 12.

Wadannan kauyuka da aka ruwaito wai sune za a yi wa wannan dira sun hada da Kawure, Kuregbe, Awulo, da Chukuba.

Cikin sa’a guda da wallafa labarin mutum 500 sun yaba da abinda ya wallafa wasu kuma mutum 422 cikin masu karatu suka yada wannan magana na Adedetu. Mafi yawa daga cikin wadanda suka tofa albarkacin bakin su kan wannan sako sun dorawa shugaba Muhammadu Buhari da gwamnatin shi laifi.

Tantancewa

Dubawa ta fara bincike daga shafin google domin gano jihohin da ke amfani da sahri’ar musulunci tukunna. Binciken ya nuna shafin jaridar The Pulse.ng wadda ta yi wani labari mai taken “Abubuwa hudun da ya kamata a sani dokar sahri’ar musulunci a Najeriya. Jaridar ta kuma jera sunayen jihohin da ke amfani da dokar shari’ar kamar haka: Zamfara, Kano, Sokoto, Katsina, Bauchi, Borno, Jigawa, Kebi, Yobe, Kaduna, Neja da Gombe.

Binciken ya kuma nuna cewa tun shekara ta 2000 aka kaddamar da shari’a a jihar Neja lokacin mulkin tsohon gwamna, marigayi Abdullahi Kure.

Da muka takaita binciken zuwa abubuwan da ke faruwa yanzu a jihar musamman dangane da ayyukan Boko Haram, wadanda aka wallafa a jaridar Vanguard, inda gwamnan jihar Abubakar Bello, cikin watan Afrilun 2021 ya yi kukan cewa Boko Haram ta shiga yankunan jihar ta sanya tutocinta a wasu kauyuka ciki har da kauyen Kaure da ke karamar hukumar Shiroro suka kuma raba wasu daga cikin matan da suka rasa matsugunnensu tsakaninsu domin su kasance matansu na karfi da yaji.

A jawabin da ya yi lokacin da ya kai ziyara sansanin wadanda suka rasa matsugunnen su da ke makarantar firamaren IBB kusa da fadar sarkin Minna, gwamna Bello ya ce sakamakon tudadowar da wadanda suka rasa matsugunnen su a kauyuka ke yi, gwamnati ta mayar da makarantar sansanin masu neman matsugunni domin samar da kulawa ga wadanda abin ya shafa.

A cewar gwamnan, “ Sambisa na da tazarar kilomitoci da yawa daga Abuja, amma kilomita 2 ne kacal daga Kaure zuwa Abuja, inda ya jaddada cewa ba wanda ke da tabbacin tsaro.

“ Kowa na iya ganin tutar da suka sa a kauyen Kaure da ke karamar hukumar Shiroro ” ya ce.

Shi kan shi shugaban karamar hukumar Shiroron ya bayar da tabbacin hakan a wata hirar da ya yi ranar 1 ga watan Oktoba 2021 inda ya ce al’ummomi 500 a unguwanni 8 da ke karamar hukumar na karkashin jagorancin Boko Haram. Kafofin yada labarai irin su Channels TV, The Nation, The Cable, YouTube da sauransu duk sun dauki labarin.

Ya bayyana sunayen yankunan da abin ya shafa, kuma sun hada da Manta, Gurmana, Bassa-Koki, Allawa, Kurebe, Kushaka, Kwai, Chukuna da Galadima Kogo.

A cewarsa ‘yan ta’addan sun yi yunkurin jan ra’ayin wasu daga cikin mazauna al’ummomin su zo su yi aiki da su. Wani Mr Chukuba wanda ya yi Allah wadai da wannan lamarin y ace ‘yan ta’addan suna neman yi wa mutane dammara ne su yaki gwamnati.

“ Suna jan ra’ayin mutane a al’ummomin suna gaya musu cewa suna da makamai da kudin da za sub a su idan suka taimake su wajen yakar gwamnati,” ya ce.

Duk da cewa ‘yan ta’addan sun shiga wadannan al’ummomin, babu wanda ya tabbatar da zargin cewa an sanya dokar shari’a bare ma a aurar da ‘yan mata masu shekaru 12 na haihuwa.

A Karshe

Bisa ga hujjojin da muka samu, zargin cewa Boko Haram ta kafa dokar shari’a a wasu kauyukan da ke kararmar hukumar Shiroro har ma ta ce za ta aurar da yan mata masu shekaru 12 auren dole karya ne.