Babban ɗan Ganduje ya kai mahaifiyarsa Hafsat Ganduje EFCC

Uwar gidan Gwamnan jihar Kano Farfesa Hafsat Abdullahi Ganduje ta ƙi amsa gayyatar hukumar yaƙi da rshawa EFCC biyo bayan maka sunan ta da babban ɗan gwamnan jihar, Abdulaziz Umar Ganduje ya yi a gaban hukumar. Yana zargin ta da yin almundahana da kuma azurta kanta ta hanyoyin da basu dace ba.

  • Babban ɗan Ganduje ya kai mahaifiyarsa Hafsat Ganduje EFCC
  • Da Ɗumi-Ɗumi: Ƴan bindiga sun sace wani Sanata

Jaridun Premium Times da Daily Nigerian sun ruwaito hukumar EFCC ta aikewa da Hafsat Ganduje sammacin zuwa gabanta ta amsa tambayoyi kan zargin amma taki amsa gayyatar, ba tare da ta bayar da wani uzuri a rubuce ba.

A cikin wasiƙar ɗan nata Abdulaziz Umar Ganduje ya tura wa EFCC ta shafi badaƙalar filaye da kuma kuɗaɗe.

An wallafa wannan Labari September 13, 2021 9:49 PM