DAMBARWAR ƊA DA UWA: Abdulazeez Ganduje ya maka mahaifiyarsa Hafsat Ganduje a hukumar EFCC

A wata sabuwar harkalla tsakanin dan gwamnan Kano Abdullahi Ganduje da mahaifiyar sa Hafsat ganduje ya kai ga hukumar EFCC na neman mai dakin gwamnan ruwa a jallo kan karar da danta ya kai hukumar EFCC na hannu dumu-dumu da take da shi wajen kumbiya-kumbiyar waskewa da wasu miliyoyin nairori da dubban daloli.

PREMIUM TIMES ta gano cewa Abdulazeez Ganduje ya kai karar mahaifiyar sa Hafsat Ganduje hukumar EFCC yana neman ta dawo da wasu kudaden harkallar filaye a Kano da ya bata wanda wasu dake bukatar gwamnatin mahaifin sa su mallaka musu filayen.

A wasikar wanda PREMIUM TIMES ta yi wa ganin kwakwaf, ta hango Abdulazeez ya rubuta cewa wasu masu neman wannan filaye sun bashi dubban daloli da naira har miliyan 35 domin gwamnati ta mallaka musu wasu filaye a Kano.

Daga baya ba kuma ba a basu filayen ba, a ka yi musu yankan baya aka rabawa wasu, shine suka bukaci a biya su kudaden su.

PREMIUM TIMES ta gano cewa shi Abdulazeez kamar yadda ya rubuta, mahaifiyarsa ya danka wa kudaden.

Dama kuma dai akwai kwanton harkallar daloli da da ta yi wa Lauje a ka, wanda a dalilin kariya da yake dashi na gwamna ya sa hukumar EFCC ta yi shiru akai, duk da ya karyata wannan harkallar da aka ganshi kurukuru yana zura daloli a aljifan jamfar sa.

Ita Hafsat Ganduje ba ta da irin wannan kariya, saboda haka akwai yiwuwar ta garzaya EFCC, duk da ko ta kaucewa kiran hukumar a wannan karon.