Ba ayi zabe a Katsina ba, coge aka yi kuma za mu garzaya Kotu – Lado-Danmarke

Jami’yyar PDP ta yi watsi da sakamakon zaben gwamnan da aka gudanar ranar Asabar din da ta gabata a jihar Katsina tana mai cewa tabbas za ta garzaya kotu.
Darekta Janar din Kamfen din dan takarar gwamnan jihar Lado, Mustapha Inuwa ne ya sanar da haka a taron da ya yi da manema labarai ranar Litini a garin Katsina.
Idan ba a manta ba bisa ga sakamakon zaben da hukumar zabe INEC ta sanar dan takarar jami’iyyar APC Dikko Radda ne ya lashe zaben gwamnan jihar Katsina da kuri’u 859,892.
Radda ya doke abokin takarar sa Yakubu Lado-Danmarke na jami’yyar PDP wanda ya samu kuri’u 486,620.
Inuwar ya ce sakamakon zaben ba shi bane zabin mutane ba.
“Ba a yi zabe a jihar Katsina ba. Muna so mu sanar da ku cewa ba tare da wani shakka ba cewa mun yi Allah wadai da sakamakon zaben da aka bayyana na zaben ranar Asabar 18 ga Maris 2023.
“An gudanar da zaben tare da tsoratarwa da cin zarafin mutane da dai sauran munanan aiyukkan da suka saba wa dokar zabe.
Ya Kuma ce an hana magoya bayan PDP jefa kuri’a musamman a rumfunar zaben da aka san jami’yyar ta fi yawan magoya baya.
“A dalilin haka ya sa muke so mu sanar cewa mun yi watsi da sakamakon sannan za mu garzaya kotu.