ZAƁEN KANO: Ganduje, Gawuna Garo da APC sun ƙi amincewa da sakamakon zaɓe, sun yi zanga-zanga a Kano

Jam’iyyar APC ta ƙi amincewa da kayen da NNPP ta yi mata a zaɓen gwamnan Jihar Kano, wanda Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana Abba Kabir na NNPP ne ya yi nasara kan Nasiru Yusuf na APC.
APC ta ce bai wa Abba nasara da INEC ta yi, ya kauce wa Dokar Zaɓe ta 2022.
Shugaban APC na Jihar Kano, Abdullahi Abbas ne ya bayyana wa manema labarai haka a ranar Talata, inda ya shaida masu cewa INEC ta yi babban kuskure da ta bayyana Abba a matsayin ɗan takarar da ya yi nasara.
Abbas ya ce tuni har APC ta rubuta wa Hedikwatar INEC ta Ƙasa wasiƙar ƙorafi, a ƙarƙashin Sashe na 65 na Dokar Zaɓe ta 2022.
Ya ce APC na so a soke nasarar Abba Kabir ta bayyana zaɓen cewa ‘inkwankilusib’ ne. Kuma sun nemi a soke nasarar a yi ‘inkwankilusib’ cikin hanzari.
INEC ta bayyana NNPP ta samu 1,019,602, APC kuma 890,705.
Baturen Zaɓe Farfesa Ahmad Doko ya ayyana Abba Kabir na NNPP cewa shi ne ya yi nasara.
Sai dai kuma APC ta ce ba a yi daidai ba, kamata ya yi a ce za a yi ‘inkwankilusib’, idan aka yi la’akari da yawan ƙuri’un da aka soke.
INEC ta tattara yawan ƙuri’un da aka soke sakamakon aringizo da tarzoma sun kai a faɗin jihar lokacin zaɓe sun kai 273,442. Wato sun nunka adadin yawan ƙuri’un da Abba ya yi wa Gawuna rata da su guda 128,897.
Su APCn da Gawuna suna Ƙorafi ne akan ƙuri’un da suka ɓaci ta hanyar fasa akwatuna da ɓatattun ƙuri’u, da suke ƙorafin sun kai adadin dubu 273,442.
A bisa kallon yawan adadin ƙuri’un da waɗannan akwatuna suke ɗauke da su.
To don haka sai APC da Gawuna su ke so Baturen Zaɓe, ya kalli yawan adadin da mutanen da suka yi rijista a dukkan akwatunan da aka soke ƙuri’un su ya bayyana sakamakon a matsayin bai kammala ba, wato ‘inkwankilusib’.
A ɗakin tattara sakamakon zaɓen ma wakilin APC Rabi’u Suleiman Bichi ya yi wannan ƙorafin.
Sai dai Baturen Zaɓe ya yi masa bayani da cewa:
“Doka ta ba shi dama ya yi amfani da doka ɗaya daga cikin biyun nan:
1. Doka ta ce zai iya lura da adadin ƙuri’un ɗin da BVAS ta tantance ya yi hukunci.
2. Ko ya yii amfani da yawan ƙuri’n da aka yi rajista, a akwatunan da aka soke.
To shi ya yi amfani da ta farko, ya kalli adadin ƙuri’un da BVAS ta tantance.Don haka idan aka kalli adadin yawan ƙuri’un da aka yi nasara, aka kuma auna da yawan ƙuri’un da aka soke, sannan aka kalli adadin akwatunan da waɗanda BVAS ta tantace aka janye ɓatattun ƙuri’un, to za’a ga Abba ya yi nasara da ƙuri’a dubu talatin da ‘yan kai.