ANA WATA GA WATA: Safara Da Harkallar Hodar Ibilis: Hukumar NDLEA na farautar Abba Kyari ruwa a jallo

A wata sabuwar harkallar da safarar muggan kwayoyi da hukumar NDLEA ta bankaɗo an sami babban ɗan sanda Abba Kyari da hannu dumu-dumu cikin jigila da kasuwancin su tun daga Najeriya har kasar Brazil.

Idan ba a manta ba Kyari na cukuikuye har yanzu cikin badaƙalar cin hanci, almundahana, zamba da yaudara wanda rikakken dan damfara Hushpuppi ya fallasa shi

Sai dai kuma a wancan lokaci Kyari ya musanta hannu da ya ke da shi a harkallar, yana mai cewa ɗinkin jamfa ne ya haɗa shi da Hushpuppi ba abinda aka zarge shi da shi ba.

A doguwar takardar da hukumar NDLEA ta fitar ranar Litinin, hukumar ta bayyana ta ce ta gano ashe Abba Kyari ƙasurgumin mai safarar muggan kwayoyi ne sannan ashe yana daga cikin gaggan ƴan kungiyoyin masu safara da harƙallar muggan kwayoyi na duniya daga Brazil-Ethiopia-Najeria.

A wurin taron manema labarai da hukumar ta yi a Abuja hukumar ta ce:

” Abba Kyari da kanshi ya nemi wani jami’in hukumar NDLEA din domin su tattauna wani muhimmin magana kamar yadda ya shaida masa a waya. Bayan sun haɗu bayan sallar juma’a a wannan rana. Sai Abba Kyari ya fara bayanin cewa jami’an sa sun kama wani kasurgumin mai sfara munggan kwayoyi a Enugu. Amma abinda ya ke so shine zai damka wannan mutum ga hukumar NDLEA, amma kuma yana son maimakon a baiwa hukumar tarin hodar ibilis din da aka kama shi da su, yana so ne a raba. Ya dibi wani abu ya bai wa hukumar wani abu.

” Da jami’in mu ya sanar da hukumar abinda ake ciki sai muka ce ya ci gaba da tattaunawa da Abba Kyari har sai an kai karshe.

Hukumar ta ce daga nan sai Abba Kyari ya rika ganawa da wannan jami’i amma kuma bai sani cewa duk abinda suke yi ana ɗauka ba saboda yadda da yayi da jami’in

” Abba Kyari har kuri ya ke cewa yana kula da jami’an sa babu matsala ta ɓangaren sa. Yanzu dai za a raba hodar ibilis din gida biyu, zai ɗauki rabi ya kawo hodar ƙarya a saka ya cike wanda aka ɗiba. Kilogiram 15 da ya ɗiba an raba wa waɗanda suka fallasa harƙallar, da jami’an da suka yi aikin cafke mai safarar.

” Bayan haka sai Kyari ya nemi ya aiko da kuɗin da zai biya na hodar amma kuma jami’in NDLEA ɗin ya ce lallai sai dai su haɗu ido na ganin ido. Da Kyari yazo sai suka shiga cikin mota amma kuma motar duk an sassaka mata na’urar ɗaukan hoto, bidiyo da murya.

Hukumar ta ce ta nemi Kyari ya bayyana a gabanta domin ya kare kansa amma ya ki, shi ne ya sa hukumar ta bayyana shi ‘WANTED’.