Ana Ci Gaba Da Fuskantar Dogayen Layuka A Gidajen Mai Na Najeriya

A lokacin da ake gab da gudanar da zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi a Najeriya, karancin man fetur na ci gaba da ci wa ‘yan kasar tuwo a kwarya, da hakan zai iya zama matsala wajen yin tafiye-tafiye zuwa jihohi don gudanar da zaben.