ZAZZABIN LASSA: Mutum 40 sun kamu, 5 sun mutu cikin kwanaki 7 a Najeriya

Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC ta bayyana cewa a cikin mako daya daga ranar 27 ga Fabrairu zuwa biyar ga Maris mutum 40 sun kamu da cutar zazzabin lassa sannan cutar ta yi ajalin mutum biyar a kasar nan.

An gano wadannan mutane a jihohin Bauchi, Ondo, Taraba, Edo da Ebonyi.

Bisa ga rahoton da hukumar ta fitar ranar Talata NCDC ta ce a mako na 9 kasar ta samu raguwa a yaduwar cutar daga mutum 59 zuwa mutum 40 a mako na 8.

Zazzabin lassa

Zazzabin Lassa cuta ce da ake kamuwa da ita a dalilin cudanyar bera da abincin da muke ci. Wannan cuta dai a sannu a hankali tana ta afkawa mutanen kasar nan.

Ya kan yi wahala a gano cutar a jikin mutum domin ya kan dauki tsawon kwanaki shida zuwa 21 kafin ta bayyana a jikin mutum.

Za a iya kamuwa da wannan cuta idan aka yawaita zama tare da wanda ya kamu da cutar kuma ba a gaggauta neman magani ba.

A yanzu haka duk shekara sai cutar ta sake bayyana inda mutane da dama ke kamuwa kuma da dama ke rasa rayukansu a dalilin cutar.

Rahotanni sun nuna cewa ma’aikatan kiwon lafiya na cikin hadari wajen kamuwa da cutar musamman yadda su ne ke kula da wadanda suka kamu.

Hukumomin kiwon lafiya da kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta yi kira ga ma’aikatan kiwon lafiya da su rika kula wajen kare kansu a lokacin da suke kula da mutanen da suka kamu da cutar.

Sannan idan aka kwantanta yadda cutar ke yaduwa za a ga cewa mutane sun fi kamuwa da cutar a wannan shekaran fiye da kowacce shekara a baya.

ALAMUN KAMUWA DA ZAZZABIN LASSA.

Ciwon kai: Yawaita fama da ciwon kai alama ne cewa lallai sai an duba mutum a asibiti, domin idan zazzabin lassa ta kama mutum ciwon kai na daga cikin alamun dake fara nunawa.

Zazzabi: Za a rika jin jiki yayi nauyi kamar zazzabi-zazzabi haka idan Lassa ta shiga jikin mutum. Zazzzabi ko masassara zai rika damun mutum a wannan lokaci.

Ciwon jiki: Jikin mutum zai rika yawan yi masa ciwo matuka. Ko ina zai rika jin ciwo yake masa. Hakan ma alama ce dake nuna an kamu da Lassa. Hakna kuma sun hada da ciwon gabobin, ciwon baya, yawan gajiya sannan a wasu lokutan har da ciwon kafafu.

Amai: Saboda zafin zazzabi da ciwon kai mutum kuma zai rika yawan yin amai.

Rashin iya cin abinci: Zazzabin lassa na hana mutum iya cin abinci. zaka ci gaba daya baka bukatan cin wani abu duk ko da cewa zaka rika jin yunwa.

Yawan yin Bahaya: Za a yi fama da yawan shiga bandaki a dalilin kamuwa da wannan cuta sannan hakan zai sa mutum yawan jin kishin ruwa.

Yawaita Suma: Idan har mutum ya kamu da wannan cuta, za a rika yawan suma saboda rashin lafiyar dake jikin mutum.

Jini: Za a rika zubar da jini ta wasu kafafen jiki musamman idan abin ya fara nisa ba a duba mutum a asibiti. Hakan na nuni cewa cutar ta fara yi wa mutum mummunar illa.

YADDA ZA A GUJEWA KAMUWA DA ZAZZABIN LASSA

1. Tsaftace Muhalli: A rika tsaftace muhalli a ko da yaushe. A kau da datti a kowani lokaci sannan a rika goggoge wuarare.

2. Zubar da Shara: Idan aka tara datti, kada arika barin su kusa da gida. A kai su can wajen da ake zubdawa a nesa ko kuma a rika konawa.

3. Killace Abinci: Yin haka zai taimaka wajen hana bera ko kwari shiga cikin abincin.

4. Dafa Nama: Kafin a dafa nama kamata a rika wanke shi da ruwan gishiri domin kashe duk wasu kwayoyin cuta dake jikin naman. A tabbatar naman ya dahu sosai kafin a ci.

5. Namun Daji: A nesanta kai daga yin mu’amula da namun daji musamman jinsin berayaye da birai.

6. Cin ‘ya’yan itatuwa: Kafin a ci ‘ya’yan itatuwa ko kuma ganye a rika wanke su sosai. Hakan na kau da datti a jikin su.

7. A daina barin dabbobin gida na shiga inda ake aje abinci: Kaji da wasu dabbobin da ake kiwon su a gida kan yi mu’amula da beraye a lokutta da yawa.

8. Toshe kafafen da suka bude: A tabbatar an toshe ramin da bera zai iya shiga cikin dakunan mu.

9. Tsafta: A yawaita wanke hannaye da ruwa da sabulu kafin da bayan an ci abinci sannan idan an kammala amfani da ban daki.

10. Ma’aikatan kiwon lafiya su tabbata sun nemi magani da zarar allurar da suka yi amfani da shi a jikin wanda ke dauke da cutar ya soke su.

11. Kona daji: Kona daji na daga cikin hanyoyin dake koro beraye zuwa cikin gidajen mutane. A rika kiyayewa wajen kona dazukan dake kewaye da mu. Mai makon haka a rika feshin magani.

12. Wanke gawa a cikin Daki: Shima hakan na da illa matuka. Maimakon a rika wanke gawa a cikin gida a rika yin sa a waje ne ko kuma inda ya kamata.